Ga duk wanda ya ke bibiyar mas'alar kazafi da aka yiwa Shaikh Abduljabbar Shaikh Muhammad Nasir Kabara akan kalmar da ba zan iya furta ta akan harshe na ba zai tabbatarwa da kansa cewa wannan mas'ala shiryayya ce wacce aka kirkire ta karkashin tubali na hassada da kiyayya da gaba da adawa ta siyasa.

Sheikh Askiya Sheikh Nasiru Kabara

Duk wanda ya san Shaikh Abduljabbar sama da shekara 30 ya san shi akan gwagwarmayar dasa kaunar Shugaba S.A.W. da ba shi kariya da daukaka alkadarinsa. 


Abu ne sananne taken Shaikh Abduljabbar KOWAYE ANNABI YA FI SHI. An kai ga jallin da duk sanda wani ya taba Annabi S.A.W. kowa jira yake ya ji irin martanin da Shaikh Abduljabbar zai mayar jama'a su sami gamsuwa. 


Shaikh Abduljabbar ya yi shuhura akan gwagwarmayar kare janibin Annabi S.A.W. ba a Nigeria ba a daukacin Duniyar Musulunchi. Hasali ma akan wannan kudiri na sa na ba sani ba sabo akan Annabi S.A.W. aka sami wasu wadanda ba sa kishin Annabi S.A.W.,  wadanda mutuncinsa bai dame su ba akan biyan ta su bukatar, wadanda ba sa jin kunyar yin karya da sharri, wadanda suka kware wajen iya yin kazafi suka sami karatuttukansa suka daddatse maganganu suka shirya abin da suka yi niyyar yi suka ambace shi da wai cin zarafi ga Annabi S.A.W. ( wal'iyazu billah) karkashin gungun wasu mutane wai da suke ambaton kansu da malamai tare da jagorancin gwamnatin jihar Kano.


Idan ka dauki bangarorin da suke cikin wannan maja za ka samu kowanne bangare akwai dalilinsa na shiga wannan maja inda suka hadu akan mummunan kudirinsu akan Shaikh Abduljabbar.  


Akwai wanda rigima ce ta cikin gida da yake ganin Shaikh Abduljabbar ya zame masa karfen kafa, muddin yana nunfashi to barazana ce a tare da shi saboda irin budi da Allah ya yi wa Shaikh Abduljabbar na ilimi mamako da jawuwar matasa izuwa gare shi. Sannan kuma da mas'alar kisan dan'uwansa Shaikh Aliyul Khauwas wanda Shaikh Abduljabbar yake zarginsa akai. Akwai wadanda suke ganin cewa Shaikh Abduljabbar yana taba musu Shehi wajen ba da kariya da yake yi wa Annabi S.A.W. Wasu kuma suna ganin Shaikh Abduljabbar ya hana su rawar gaban hantsi wajen yada akidarsu ta inda yake musu taba rigarka in ka isa da ruwan hujja. Wasu ko tsabar kiyayya ce da gaba da suke yi wa gidan Shaikh Nasir Kabara suke ganin dama ta samu da sa zu kawo dauki wajen rushe kima da alkadarin wannan gida mai alfarma a idon Duniyar Musulunchi domin taba Shaikh Abduljabbar kamar taba Shaikh Nasir Kabara ne. Ita kuwa hajiya gwamnati magana ce ta faifan Dala da inconclusive da malamin ya tsaya a bayan gaskiya ya zabi ya kubuta a gun Allah ya tsira da mutumcinsa akan dan tamanin Duniya da bai wuce hudusun fana'un ba. Wa su kuma cewa suka yi yana taba manya ba shi da kunya.


Wadannan su na daga cikin manyan dalilan da suka sa wadannan mutane ma su akidu daban-daban suka kifu akan wannan bawan Allah shi daya tilo suke amfani da gwamnati dan su ci zarafinsa, su bata masa suna, idan sun sami yadda suke so ma su kawar da shi daga dorin kasa, kai ka ce su zama za su yi su dawwama a Duniya.


Dalilai da suke nuni izuwa cewa gwamnati ba ta shiryi yin adalci a cikin  shariar Shaikh Abduljabbar ba:


1. Tun farko dama ba a taki gaskiya a cikin wannan al'amari ba. Abu ne aka shirya shi da gangan dan cimma wata bukata ta kashin kai aka fake da guzuma dan a harbi karsana. Maganar zagi ko batanci ga Annabi S.A.W. karya ne! Kazafi ne! Sharri ne! Kage ne! Da gwamnati ta shiryi yin adalci a cikin wannan sharia da tun farko ba ta goyu da bayan wadannan mutane ba akan karairayin da suka shirya ba, da ta sa an nemo mata  cikakken karatuttukan da aka daddatse na Shaikh Abduljabbar ta sa ta ji da kunnen ta dan bin umarnin Ugangiji S.W.T. da yake cewa idan fasiki ya zo muku da labari to ku bincika dan kar ku zalinci mutune bisa jahilci ku wayi gari kuna ma su nadamar abin da kuka aikata. A maimakon haka sai aka dakko wannan kirkirarren sauti aka rika yada shi a kafafen yada labarai dan bata suna da yada propaganda a tsakanin al'umma, aka rufe masa masallaci aka hana saka karatunsa a kafafen yada labarai akan zargin da magautansa suka kulla masa ba da bincike ba ba da wani hukunci daga kotu ba saboda gwamnati tana da interest a kai. 


Hikimar haka shi ne a rufe bakinsa ta yadda sakonsa na gaskiya ba zai bayyana ba dan kar ya wanke wadancan karairayi da ake yadawa.


Wannan shi ne rashin adalci na farko da gwamnati ta yiwa Shaikh Abduljabbar.


2. An shirya mukabala akan za a tattara malaman Nigeria baki daya dan su yi masa taron dangi su hadu su kure shi a sako kai tsaye Duniya ta na ji sai aka ga abin ba zai yiwu ba saboda duk malaman da ake gani sun isa musamman wadanda suka shige gaba wajen wannan kazafi suna jin tsoron arangama da shi saboda su ma sun san ba su taki gaskiya ba.


Daga baya aka canja salo aka shiryo wata kitimirmira aka  tsara tuggu wai da sunan mukabala, amma abin mamaki wannan karon sai aka ce ba za a saka kai tsaye Duniya ta ji ba sannan kuma ba za a bari Shaikh Abduljabbar yazo da mutanensa su dauka ba. Kai daga jin wannan ka san akwai lauje cikin nadi. Suka kuma maimaita abin da suka yi na datse-datse suka rika sako abin da suka ga ya yi musu dadi aka rika yadawa a kafafen yada labarai. Wani abin da ba kowa ya sani ba Malam Abduljabbar shi yayi nasara a zaman wannan tuggu da aka kira da mukabala, rashin sako cikakken zaman kai tsaye shi yasa wasu ba su san haka ba.


Wannan shi ne rashin adalci na biyu da gwamnatin jihar Kano ta yi wa Shaikh Abduljabbar.


3. Bayan kama Shaikh Abduljabbar da gwamnatin Kano ta yi ta hanyar da ta saba ka'ida da gurfanar da shi a kotu ba bisa ka'ida ba, Duniya ta shaida cewa lawyoyin gwamnati da 'yan maja wadanda suka shigo ta haramtacciyar hanya sun gaza wajen kawo kwararan hujjoji da za su tabbatar da cewa Shaikh Abduljabbar ya aikata laifin da suke zargin sa da shi ta hanyar shaidun zur da suka kawo, duk da rashin cikakkiyar dama da ba a ba shi ba ta kare kansa, Duniya ta tabbatar da cewa Shaikh Abduljabbar bai aikata laifin da gwamnati da malamam maja suka kakaba masa ba. Kowa ya ji abin da ya faru a kotu adaidai lokacin da Shaikh Abduljabbar ya tsaya akan matsayinsa na bawa janibin Annabi S.A.W. kariya da nisanta shi ga barin duk wani abu da bai kamace shi ba su kuma lawyoyin gwamnati sai suka buge da tabbatarwa Annabi S.A.W. munanan kalamai marasa tushe da asali da aka ruwaito su a wasu littattafan Hadisi har suna kafa shaidu akan hakan.


Wani abin ban sha'awa, mai dokar bacci sai ga shi ya buge da likimo, 'yar burun-burun din da suka yi na cewa maganar da Shaikh Abduljabbar yayi ta kore jinginawa Annabi S.A.W. abin da bai kamace shi ba wai lafazin bai zo ba a littattafan Hadisi dan haka kenan shi ya kirkiri wannan magana. Allah rahimi sai ga shi gwamnati da malaman maja a gaban kotun shari'ar Musulunchi ta kofar kudu karkashin jagorancin mai shari'a Ibrahim Sarki Yola sun jinginawa Annabi mummunar kalma ta ZINA ( Wal'iyazu billahi) kamar yadda yazo a cikin kunshin tuhumarsu da suke yiwa Shaikh Abduljabbar dan ba bu inda ya ambaci lafazin zina, su suka kirkire shi.


Wannan shi ne rashin adalci na uku da aka yi wa Shaikh Abduljabbar.


Dan haka yanzu kallo ya koma sama, Duniya tana jira ta ga ko kotu za ta yankewa gwamna GANDUJE da MALAMAN MAJA da LAWYOYINSU hukunci daidai da yadda Shari'ar Musulumchi ta tanada sakamakon jinginawa Annabi S.A.W. kalmar batanci da suka yi ta sallami Shaikh Abduljabbar sakamakon tsayawarsa a kuto ya kare janibin Annabi S.A.W. daga dukkan abin da bai kamace shi ba ko kuwa!


Idan haka ba ta samu ba to Duniya tana zira ido ta ga an yi adalci an sallami Shehin Malamin sakamakon abin da ya bayyana a kotu na barrantarsa ga buran abin da Malaman Maja suka jingina masa.


Wani abin da ya dau hankali shi ne a wannan karon an ce za a sako zaman yanke hukunci kai tsaye sabanin abin da ya faru a baya. 


Abin tambaya anan shi ne, shin gwamnati ta yi haka ne dan ta nunawa Duniya cewa za ta yi adalci ke nan? 


Idan haka ne to me yasa a zaman mukabala ba a saka kai tsaye ba har aka hana Malam Abduljabbar ya je da wanda zai daukar masa??


Me yasa ba a saka zaman kotu da aka yi na sauraren Shariar kai tsaye ba har aka hana 'yan jarida da media team na Shaikh Abduljabbar su rika daukar zaman kotu?


Hakan yana nuna cewa kenan ba a so Duniya ta san hakikar abin da yake faruwa na gaskiya  kai tsaye a wannan lokaci dan kar a fuskanci ina gaskiya ta ke sai abin da aka yi editing aka saka?


Wannan shi ya nuna cewa lallai akwai wata manufa da ake son cimma ta saka zaman kotu kai tsaye watalika ta siyasa da kyautatawa magoya bayan malaman maja dan su rama biki ranar zabe.


Wannan ba abin mamaki ba ne idan muka yi la'akari da irin katsalandan da gwamna Ganduje ya rika yi tun daga farkon wannan al'amari ta inda ya fito ta kafafen yada labarai ya ce ya bawa kotu umarni da a dakko Shaikh Abduljabbar daga hannun 'yansanda a kai shi kurkuku.


Sannan kuma dama tun farko ya riga ya gama yanke hukunci inda ya bayyana wa Duniya cewa za su kai Shaikh Abduljabbar mayanka.


Dan haka ba abin mamaki ba ne idan gwamnati ta nuna rashin adalci a cikin wannan shari'a tun da dama ba a dakko asalin maganar bisa gwadabe na adalci ba. Kuma akwai abin da ake so a cimma dan farantawa wasu mutane.


Duk da haka muna yi wa kotu zato na Alkhairi kasancewar ta gidan adalci, idan mutum biliyan suka tsaya a gaban ta suna kalubalantar mutum guda idan ta bayyana mutum guda din nan shi ne akan gaskiya ya wajaba kotu ta tabbatar masa da gaskiyarsa, shi yasa aka cewa idon kotu a rufe yake.


Amma koma menene Duniya ta na gani kuma Allah ya na gani dan shi ne Ahkamul Hakimeena, kuma ba ya bacci.


Daga karshe kiran da nake yi ga 'yan'uwa da almajirai da masoya da abokan arziki na Shaikh Abduljabbar Shaikh Muhammad Nasir Kabara shi ne a dukufa kan Addu'a, mu mayar da lamarinmu izuwa ga Allah mahaliccin kowa da komai, idan ya ga dama sai yayi amfani da sunansa na Alqahharu ya rankasa zukatan ma su ruwa da tsaki gaskiya ta bayyana, irin yadda ya kubutar  da Annabi Musa daga hannun Fir'auna ya gama karkashe jarirai akan mulkinsa ya dauwama daga karshe Allah ya cika alkawarinsa ya halakar da Fir'auna Annabi Musa ya zo ya tsaida sakon Allah a bayan kasa.


Muna rokon Allah alfarmar wanda Shaikh Abduljabbar ya ke karewa yake daukaka martabarsa Shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W. ya Allah ka ba shi nasara mabayyaniya da rinjaye a cikin wannan shari'a Ameen