Ku duba, wannan wani Dattijo ne da ya ɗauko uwayensa daga wani ƙauye dake Jihar Zamfara. Ya ɗebo su domin ya tseratad da su daga rashin albarkar ƴan ta’adda.


 Wannan kaɗan daga cikin halin da al’ummar Nigeria suke ciki kenan. Babu tsaro, ga yunwa ga baƙin talauci, makarantu sun fi ƙarfin ƴaƴan talakawa. Amma saboda rashin Imani, Malamai sun zuba Ido, sai yanzu ne za su ɗauko maganar addini, su rainawa talakawa hankali, a ƙara zabar wani “Galmaho”.


 Kowanne commercial-Sheikh da zarar ya ɗora rawani, ya je an bashi Coco-Cola da ƴan kuɗaɗe sai ya zo mambari yana brainwashing mabiyansa su zaɓi ruɓaɓɓen ɗan Takara.


A dai ji tsoron Allah!


Comr. Tariwa