Bola Tinubu ya ce, da gangan aka ƙirƙiro wahalar man Fetur, kuma da gangan aka sake fasalin kuɗin Najeriya. Ya ce an yi haka ne domin a hana shi zama shugaban ƙasa, masú wànnan ɗanyen aikin in ji shi mutanen Aréwa né. Ya ce komai wahala za su taka da kafarsu su je karbi mulki daga hannun wadanda basa so su yi.
Dazu da rana dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya ragargaji gwamnatin Buhari.
Tinubu ya yi wannan jawabin a jihar Ogun a lokacin da yaje taron kamfen a jihar. Kuma wannan jawabin nasa ya yi shi da yaren Yarbanci. Dama a jawabin da Bola Tinubu ya yi wa shugaban kasa gori a watan Yuni da ya gabata, ya yi shi ne da Yarbanci kuma a jihar Ogun inda ya ce wannan mulkin na Yarbawa ne, kuma a Yarabawan ma na Bola Tinubu ne wato Emi lo kan.
Wanda yake jin Yarbanci ya saurara da kyau. Shin da wa Tinubu yake wannan maganar.
- Bello Muhammad Sharaɗa.
0 Comments
Post a Comment