“Ƴan iskan gari, wanda muka Samu  tabbacin cewa; Aksarinsu Matasane sun aukawa mabiya Shi'a a garin Kano Kwanan Dala a jiya Asabar Suna tsaka da gudanar da gwanon Maulidin Nana Faɗima (AS).


“Rahotonmu yace; Mabiya Shi'ar bayan sun hau sahu suna tafe suna rera waƙen yabo ga ɗiyar Manzon Allah (SAW) nana Faɗima (AS) domin tunawa ranar Haihuwarta, ba zato  bare tsammani a dai-dai kwanan Dala  ga wasu Matasa ɗauke da duwatsu wasu da gaggan Makamai suka shiga jifan mabiya Mazhabin Shi'ar mata da maza yara da manya tare da Sara Suka kan mai uwa da wabi.” 


“Har ila yau, ALFIJIR HAUSA ta cigaba da bin diddigi Kan lamarin, sai dai Wakilinmu ya tabbatar mana cewa; a Sanadiyar wannan aukawar da waɗannan ƴan iskan gari sukayi akan Mabiya Shi'a yayi Sanadiyar samun  raunuka na wasu daga cikin ƴaƴan Mazhabin Shi'ar da daman gaske.”


Bugu da ƙari ba'a rasa rai ko da na Mutum ɗaya ba.”