Sun buɗe portal ɗin ne daga farkon watan tara (September) za kuma su kulle a ƙarshen watam sha biyun nan da muke ciki (December), sun sanar da cewa, duk wanda ya applying bayan watan sha biyu ta ƙare baza su ɗauke shi ba.
Da wannan nake ƙiran ƴan uwa da cewa su yaɗa wannan rubutun domin sanarwar yaje ga ƴan uwa akan lokaci su samu su cika tun kafin lokacin ya ƙure.
Akwai ƙa'idoji da yawan gaske wajen cikewar , saboda haka nema ake so duk wanda ya shiga cikin portal ɗin ya tsaya ya natsu ya karanta da kyau kafin ya cika komai.
Akwai special requirements daga cikin requirements ɗin da ake so duk wani mai sha'awar cikewa ya mallaka ya kasance dasu kafin ya cike, gasu kamar haka-:
1). Tazkiyyah (Attestetion Letter) daga wata hukuma ta ƙasa ko kuma wani babban mutum sananne a ƙasa ta fuskar addinin Musulunci ko ta fuskar shugabanci.
2). Katin ɗan ƙasa wanda hukumar ƙasar ta tanadar.
3). Ya zamo ka iya larabci musamman ma idan kana da shahadah (Certificate) akan course ɗin larabci daga wata hukuma sananniya mai zaman kanta ko kuma ta gomnati.
4). Ya zamo ka iya turanci ta fuskar rubutu da karatu da kuma yin magana dashi, musamman ma kuma akwai certificate akan hakan.
5). Katin barin ƙasa, (Fasfo) da kuma (Biza) domin zuwa ƙasar Qatar ɗin.
Waɗannan kaɗan ne daga requirements da ake buƙata ka kasance dasu kafin ka fara cikewa, na sorting ɗinsu out ne saboda sune muhimmmai (special) daga ciki.
Ba a cikin portal ɗin ake cikewa ba, a'a!
Form ɗin za a baka, shafuka biyu ne zuwa uku, kai kuma sai ka sauƙe su a matsayin PDF kaje CAFE ayi maka priting, sai ka cike, ka haɗa da sauran dukkan abinda ake buƙata na takaddun ka sai ka tura musu ta email ɗin da suka bayar.
Kar ayi min tambaya akan yadda ake cikewan, domin nima ban fara cikewa ba, na dai karanta bayanan ne, sai dai kawai abinda na fahimta shi ne-:
Bayanan suna da yawa, dole ana buƙatar natsuwa sosai da maida hankali domin a fahimce su, anyi bayanan ne da yaren larabci, amma ga waɗanda suke amfani da browser ta Chrome zasu iya juyawa zuwa yaren Turanci domin su fahimta idan hakan zai fi musu.
Ga link ɗin da za abi domin shiga cikin portal ɗin, link ɗin shi ne a ƙasa.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://www.islam.gov.qa/inner/Scholarships
Fatan Allah ya baiwa kowa sa'a, yasa mu dace!
.
.
Ibrahim Ra'ees Abou Mous'ab
Sunday!
24/05/1444 H.
18/12/2022 M.
0 Comments
Post a Comment