Rahotanni daga babban birnin tarayyar Abuja, na nuni da cewar, jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS, sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda suka kwace ofishin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.
A watan Disambar 2022 ne wata babbar kotun tarayya a Abuja ta haramtawa DSS kama, gayyata, ko kuma tsare Emefiele, harma kuma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a ranar Talata 17 ga watan Janairu.
Jami’an na DSS sun hana duk ma’aikatan babban bankin shiga ofishin Emefiele.
0 Comments
Post a Comment