Wata babbar kotun jiha dake zaman ta a miller road Kano ƙarƙashin Mai Shari'a Amina Adamu ta yankewa wata budurwa mai suna A'isha Kabir hukuncin kisa ta rataya bayan shafe sama da shekara guda ana gudanar da Shari'ar ta bisa zargin kashe wata maƙociyar ta mai suna Bahijja Abubakar.
An gurfanar da Aisha ne bisa zargin kashe Bahijja ta hanyar soka mata wuƙa a wuya bayan saɓani da ya faru tsakanin su. Rikicin ya samo asali ne yayin da A'isha ta kira Bahijja da sunan ''Karuwa'' wanda ya kai ga rigima tsakanin su har Bahijja ta rasa ranta sakamakon wuka da A'isha ta soka mata.
A zaman kotun na yau Laraba Mai Sharia ta karanto abubuwan da suka wakana a baya cikin shari'ar, inda daga karshe kotun ta bayyana cewa ta samu wadda ake zargin da laifi kuma ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Lawyan dake kare wadda ake tuhuma Barr Auwal Abubakar Ringim ya bayyana cewa baza su ce komai ba dangane da yunkurin daukaka ƙara har sai sun zauna sunyi nazari.
''Abunda ya faru shi ne an samu sabani da ita wadda ta rasu da kuma wadda aka yanke wa hukunci, daga baya ita wadda ta rasu ita da kawayenta suka je har wajen aikin wadda aka yankewa hukuncin suka fara dukan ta sannan fada ya hargitse anan ne abun ya faru'' inji Barr Auwal Ringim.
An nasu bangaren, É—an uwan Bahijja mai suna ÆŠanlami Abbas ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da babbar kotun ya yankewa wanda ake tuhuma.
"Alhamdulillah ina godiya ga wadanda suka bayar da gudunmawar su har lokacin da aka kawo karshen wannan shari'ar, kuma mun gamsu da wannan hukuncin''
Shima Lauyan gwamnati Barr Lamido Abba SoronÉ—inki ya bayyana cewar sun gamsu da wannan hukunci da kotun ta yanke.
''Daman ita kotu, kowanne lokaci adalci ta ke yi, kuma mun gamsu da abunda da kotu ta yi, kuma muna fatan wannan zai zama izina ga sauran mutane'' inji LamiÉ—o.
Ya kuma bayyana cewa suna jiran wadanda akai ƙara idan sun ɗaukaka ƙara.
Aliyu Samba
0 Comments
Post a Comment