Askia Nasiru Kabara kani ne ga Sheikh Abduljabbar Kabara wanda kotu ta yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin batanci ga ANNABI MUHAMMAD S.A.W,  Askia ya shaidawa jaridar The Punch cewa kawai siyasa ce tasa aka yankewa Malamin hukunci.


Askia Kabara wanda yake uwa daya uba daya da Abduljabbar Kabara ya ce bai yi mamakin hukuncin da kotun shari'ar ta yanke ba.


"Ban yi mamaki kan hukuncin ba saboda shi ne abinda muka zata gwamnatin jiha zata yi, rashin adalci ne, gwamnatin Kano na da boyayyiyar manufa da take son cimmawa. Shiyasa ban yi mamaki ba da naji hukuncin".


Malam Askiya ya ce asalin batun ya taso ne daga rashin jituwar dake tsakanin Malamin da dan'uwansa, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara.


" Batun ya samo asali ne daga siyasa, akwai hannun mutane dayawa a ciki, abin ya fara ne daga rikicin cikin gida mussaman rikici da Yayana Karibullah Nasir Kabara, shi ne wanda ya hada kan Malamai wajen bata sunan Sheikh Abduljabbar ta hanyar gungun Maja wadanda suka tunkari Gwamna Ganduje da batun wanda daman yana abin cewa kan batun, daga nan suka fara shirin kawar da Sheikh Abduljabbar."


Malamin yayi kuma fatan cewa a yayin da aka daukaka kara yana fatan za a sallami, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.