Nan da 29 ga watan Maris din shekarar nan da muke ciki ne wa'adin mulkin gwamnatin tarayya da wasu daga cikin gwamnonin kasar zai kare.
Kididdigar ofishin da ke lura da basuka na Najeriya ya ce gwamnonin jihohin kasar 28 za su tafi su bar basukan da suka kai naira tiriliyan 5.8.
11 cikin jihohi 28 na gwamnonin kasar za su kara tsayawa takara a watan.
Gwamnonin da za su kara neman takara sun hada da Gwamnan Gombe Mohammed Inuwa Yahaya da na Borno Babagana Zulum akwai kuma na Nasarawa Abdullahi Sule da Seyi Makinde na Jihar Oyo na cikinsu sai Gwamnan Yobe Mai Buni.
Akwai Gwamna Bello Matawalle na Zamfara; da Babajide Sanwo-Olu na Lagos da Adamawa Gwamna Ahmadu Fintiri da Dapo Abiodun daga Ogun akwai Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da kuma Abdulrahman Abdulrazak na jihar Kwara.
Wadanda ba za su nemi tazarce ba sun hada da Emannuel Udom na Akwa Ibom da Samuel Ortom na Benue da Ifeanyi Okowa na Delta da David Umahi na Ebonyi da Aminu Masari na Katsina da Bello Bagudu na Kebbi da Abubakar Bello na Neja akwai Aminu Tambuwal na Sokoto da Simon Lalong na Plateau sai kuma Darius Ishaku na Jihar Taraba.
Sauran sun hada da Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufai da Gwamnan Kano Abdulahi Umar Ganduje da Victor Ikpeazu daga Abia sai Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Ben Ayade na Cross Rivers da kuma Nyesome Wike na Jihar Rivers.
Bashin jihohin ya rabu gida biyu na gida da ake karba daga wurin masu bayar da bashin cikin gida, sai kuma na ketare da ake karba daga cibiyoyin bayar da ba shi kamar su Babban Bankin Duniya.
Duka basukan na gida da na ketare an wallafa su a shafin hukumar da ke lura da basuka tsakanin watannin Satumba da Yunin 2022.
A cewar rahotannin, bashin da jihohin suka ci na cikin gida ya kai naira tirliyan 4.38, yayin da wanda suka karba na waje ya kai dalar Amurka biliyan 3.15 kimanin naira tiriliyan 1.42, idan an buga sauyin kudi kan farashin da gwamnati ke bayarwa na dala daya a naira 449.53.
$60.05m
Ebonyi bashin cikin gida N67.06bn na ketare $59.84m
Gombe bashin cikin gida N139.1bn na ketare $46.93m
Jigawa bashin cikin gida N44.41bn na ketare $27.61m
Katsina bashin cikin gida N62.37bn na ketare $55.82m
Kebbi bashin cikin gida N60.13bn na ketare $42.40m
Kwara bashin cikin gida N109.55bn na ketare $45.94m
Nasarawa bashin cikin gida N72.63bn na ketare $53.73m
Niger bashin cikin gida N98.26bn na ketare $69.27m
Oyo bashin cikin gida N160.07bnna ketare $76.97m
Plateau bashin cikin gida N151.90bn na ketare $33.74m
Sokoto bashin cikin gida N85.58bn na ketare $37.13m
Taraba bashin cikin gida N90.81bn na ketare $22.28m
Yobe bashin cikin gida N92.86bn na ketare $23.09m
Zamfara bashin cikin gida N109.69bn na ketare $29.33m
Abuja bashin cikin gida N112.49bn ana ketare$25.38m
'Gwamnatin Tarayya ba za ta iya hana jihohi cin bashi ba'
Matsalar bashi a Najeriya ya zama ruwan dare tsakanin jihohi da kuma gwamnatin tarayya, in ji Dr Muhammad Shamsuddeen wani kwararren masanin tattalin arziki a jami'ar Bayero da ke Najeriya.
Dr Shamsudden ya ce, wannan ya samo asali ne daga yadda Gwamnatin Tarayya ta wannan lokaci ta karbi basukan da suke neman yi mata katutu.
A 2015 da gwamnatin Shugaba Buhari ta karbi mulki bashin da ake bin Najeriya bai zace tiriliyan 12 ba.
Lokacin da aka kammala shekara hudun farko bashin ya kai tiriliyan 27 ma'ana a 2019.
A yanzu kuwa 2022, masana na cewa bashin ya kai kusan tiriliyan 44, wanda ba karamin abu ba ne ga kasar.
"Abin da gwamnatin jihohi suka ga ta Tarayya ke yi ne suma suka kwafa, kuma gwamnatin Tarayya ba za ta iya hana su karbo basukan ba, shi kansa ofishin kula da bashi na kasa ba zai iya hanawa ba.
"Bankin Duniya ya ce basukan da ake bin Najeriya sun yi yawan gaske." in ji Dr Shamsuddeen.
A karshen watan shida na 2015, in ji Dr basukan da ake bin gwamnoni bai wuce tiriliyan 1.690, amma yanzu ya kai tiriliyan 5.8, a ko wanne irin ma'auni wannan ya yi yawa, saboda an samu karin ne cikin abin da ya gaza shekara takwas.
Babbar illar da wannan bashi zai yi shi ne, barin duk wanda zai maye gurbinsu a cikin gwamnati. Hakan zai hana su sukunin gudanar da manyan ayyuka a jihohin.
Gaba daya wannan matsalar za ta kare kan 'yan kasa ne, saboda ba za a rika yi musu aikin ci gaba ba, da kuma walwalrsu.
BBC Hausa ✍️
0 Comments
Post a Comment