Hukumar yan sanda ta jihar Kano, ta sallami jigon jam'iyyar NNPP, kuma zaɓaɓɓen dan majalisar tarayya na karamar hukumar Dala dake jihar Kano, Aliyu Sani Madaki, bayan gayyatar da tayi masa a ranar Laraba, bisa bincike akan wani hoto da aka ganshi rike da Bindiga a hannunsa, yayin ziyarar da dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kawo Kano a makon jiya.


Wata majiya ta tabbatar da cewa, tuni aka sallami Madaki bayan ya shafe daren jiya a sashin binciken manyan laifuka na hukumar yan sanda ta jihar Kano dake Bompai, amma saida ya gabatar da lasisin Bindigar, da kuma tabbatar da cewa bai harbi kowa da ita ba, kamar yadda jaridar Sahelian Times ta rawaito.

A ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata ne, Kwankwaso ya ziyarci Kano domin rufe yaƙin neman zaɓensa, wanda kuma wasu yan Daban siyasa suka farmaki wasu cikin tawagar da suka tafi domin taro shi a Kwanar Dangora.

Ko a ranar ma saida yan sanda suka cafke shugabannin ƙananan hukumomin Rimin Gado da Ungogo, Munir Dahiru da Abdullahi Ramat, rike da Bindiga kirar Pistol a tare dasu.