Guda cikin 'ya'yan gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, mai suna Bashir Nasir El-Rufai, ya bayyana dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen shekarar 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wanda yafi tasiri a siyasa bayan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Bashir din ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, inda ya ce masu yiwa Kwankwaso dariya saboda iyaka jihar Kano yaci a zaɓen shugaban ƙasa, ba za suyi dariya a shekaru kaɗan masu zuwa ba, domin shi ne Buhari na gaba.
A ranar 25 ga watan Fabrairu na wannan shekara ta muke ciki ta 2023, aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, inda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC yayi nasara, ya kayar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Peter Obi na jam'iyyar LP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP da sauran yan takara.
0 Comments
Post a Comment