Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya ce Nijeriya za ta zama ba a vain ta bashin ko sisi, kuma ingantaccen ilimi zai samu idan aka zabe shi.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a taron muhawara da kungiyar haɗa muhawara yan takara da haɗin gwiwar Hukumar da ke kula da Watsa Labarai shirya a Abuja.

Kwankwaso ya ce zai tattauna batun biyan basussukan Najeriya, da inganta kudaden shiga da kuma tabbatar da cewa kudi na zuwa wuraren da su ka dace.

Hakan, in ji shi, zai sa a samu ingantattun abubuwan more rayuwa da ci gaba.

“Zan toshe duk wata hanya da kudi ke zurarewa da almubazzaranci, akwai kudi da yawa a cikin kasar wanda ya isa ya dauki nauyin komai.”

Ya ce ilimi zai inganta a karkashin sa, zai baiwa matasa tallafin karatu tare da kawo karshen yajin aiki ta hanyar biyan bukatun kungiyoyin kwadago.

“Ilimi shi ne alamar tafiyar Kwankwasiyya , mun tsaya tsayin daka wajen neman ilimi wanda shine karfin mu , ba za a samu lalalatattun ajujuwa ba .

“Kowane yaro zai je makaranta kuma za mu magance rashin zuwa makaranta na yara yara . Zan ba da fifiko ga ilimi kuma za a magance matsalar kudin jarabawa.”