A karshe jami’an zabe sun gano bacewar takardun zaɓe dubu 24,682 na mazabar Tofa/Rimingado/Dawakin Tofa a jihar Kano, bayan da wakilan jam’iyyar NNPP, su ka yi ƙi amincewa da kason da bai kammala ba.
Jami’an jam’iyyar sun yi al'ajabi kan yadda aka ɓoye biyu daga cikin katan 16 na takardun zabe kuma ba a ga guda dubu 24,682 da aka ɗebe daga cikin katan-katan ɗin.
Wani wakilin NNPP, Surajo Ahmad, ya shaida wa DAILY NIGERIAN cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta ware takardun zabe 265,182 domin gudanar da zaben mazabar, amma abin mamaki sai suka gano 240,500 a cikin akwatunan.
“Akwai kwali 16 ɗauke da takardun zabe 16,200 kowanne. Don haka a lokacin da ake tantance na mazabar tarayya ta Tofa/Ringado/Dawakin Tofa, sai muka gano cewa an kwashi wasu takardun dangwala kuri'a a akwatuna guda biyu a.
“Don haka lokacin da muka duba akwatunan da ake tuhuma, mun gano cewa jimillar katunan zabe 24,682 sun bata.
" Sai muka dage cewa ba za mu bar jami’an su dauki kuri’u da ba su cika ba. Da muka yi bincike a ko’ina a cikin CBN ba mu gani ba, sai jami’an INEC sun roke mu mu zo gobe.
“Abin mamaki, da muka zo washegari da safe, sai jami’an INEC su ka ce sun gano kuri’un da su ka bata. Abin tambaya a nan shi ne wane ne da farko ya fasa akwatunan da aka rufe kuma ya cire katin zabe? Ta yaya kuri’un su ka bayyana duk da cewa mun duba lungu da sako ba mu gansu ba jiya ?,” inji shi.
Kakakin hukumar ta INEC, Festus Okoye, bai ce komai ba lokacin da DAILY NIGERIAN ta tuntube shi kan lamarin.
0 Comments
Post a Comment