A yayin kudubar Juma'ar da ya gabatar yau a masallacin gidan tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso Shaikh Daurawa ya caccaki malaman addinin da ke amfani da mumbarinsu domin tallata 'Dansiyasa, a cewar Malam "Mumbari na Annabawa ne da ya kamata ya zama na ilmantarwa, karantarwa, wa'azantarwa da bayyana wa mutane siffofi, dabi'u da halayen da ya kamata a zabi mutum saboda su."


Sallar juma'ar wacce ta sami halartar Dantakarar Shugaban Nijeriya a jamiyyar NNPP Eng. Dr. Rabi'u Kwankwaso tare da magajinsa Abba Gida-Gida 'Dantakarar Gwamna a Kano. A cikinta Malam ya yi tsokaci game da nasiha kan zaben da zai gudana gobe asabar yana cewa lallai jama'a su sani su ababen tambaya ne kan wanda suka zaba, mafita ita ce kawai a zabi wanda ya cancanta ba wanda zai bayar da kudi ba.


Malam ya kawo hadisin Manzon Allah (SAW) da ya yi magana kan mutum uku wanda a gobe kiyama Allah ba zai yi magana da su ba, ba kuma zai tsarkake su ba, suna da azaba mai radadi. Wanda guda daga cikinsu shi ne mai zaben shugaba saboda abun duniya ba don ya cancanta ba. Idan am ba shi ya goyi bayansa idan ba a ba shi ba kuma ya bijire masa. Fadin Annabi cewa"

ﻭﺭﺟﻞ ﺑﺎﻳﻊ ﺇﻣﺎﻣﺎ ﻻ ﻳﺒﺎﻳﻌﻪ ﺇﻻ ﻟﺪﻧﻴﺎﻩ ﺇﻥ ﺃﻋﻄﺎﻩ ﻣﺎ ﻳﺮﻳﺪ ﻭﻓﻰ ﻟﻪ ﻭﺇﻻ ﻟﻢ ﻳﻒ ﻟﻪ."


Daga nan Malam ya kawo tarihin yadda ake zabe da abubuwan da ake dubawa domin zabe tun bayan wafatin Manzon Allah (SAW) har zuwa karshen khalifancin Alkhulafa'u Rashidun. Bayan haka Malam ya bayar da dalilan da ke saka wa a zabi mutum, na farko dai shi ne lafiyarsa, ilminsa, halayensa, nagartarsa, yanayinsa da abin da ya yi a baya da abin da ake tunanin zai yi a gaba.


Malam ya buga misali da 'Dalot wanda Allah ya ba shi mulki kan sauran mutane sai suka yi korafi me ya sa zai zama shugabansu alhalin ba kudi ne da shi ba sai Allah ya ce ya ba shi ilmi da lafiyar jiki wanda hakan ne dalilin ba shi mulki. Annabi Yusuf An nada shi mukami ne saboda amanarsa da kuma ilminsa. Annabi Musa sanda ya yi hijira zuwa Madyana dattijon da ya ba shi diyarsa ya aura ya dauke shi aiki ne saboda karfin jikinsa da amanarsa kamar fadin Allah cewa"

قالت إحداهما يا أبت استأجره إن خير من استأجرت القوي الأمين "


Malam Daurawa ya ce" Ku sani lallai kuri'arku amana ce da Allah zai muku tambaya a kanta gobe kiyama. Malamai sun ce daga dalilan da ake zabar shugaba shi ne don ya yi adalci ya yi tausayi da rikon amana ya kuma cika alkawarin da ya dauka. Sannan ya yi gaskiya ya kuma tsare maka addininka ya kuma ba ka ingantaccen ilmi. Inda ka dangwala kuri'arka nan ne makomar rayuwarka komai da komai. Muddin jama'a na son magance matsalolin kasar nan to sun sami dama ta hanyar zaben wanda suke ganin ya cancanta. Ilmi ya lalace, babu tsaro hanyoyi sun farfashe, asibitoci sun zama wurin dibar gawa amma duk da haka a ba ka rana daya ka yi kuskuren zabar wanda bai cacanta ba sai daga baya ka zo kana kuka kan matsalolin rashin tsaro, yunwa, kidnafin da rashin asibitoci."


"Ai ko mutanen kirki biyu ne suka fito takara a hankalce an ce a zabi wanda ya fi kirki. Idan na banza ne suka fito an ce mu zabi mai dan dama-dama, da bakikkirin gwara baki-baki. Balle abin da yake a fili Allah ya ba ka hankali da tunanin da za ka gane da kuma halin da kake ciki kana karba a jika. Mu ne dole za mu canza da kanmu Mala'iku ba za su sakko daga sama ba, don haka mu kyautata zato mu fito mu yi zabe tsakaninmu da Allah mu zabi wanda ya cancanta."


Muna rokon Allah ya zaba mana shugaba nagari.


Daga Imam Aliyu Indabawa