Kwamitin kamfen din takarar shugabancin kasa ta Rabi'u Kwankwaso, PCC, ya yi hasashen cewa dan takarar zai kayar da abokan takararsa da tsiran sama da kuri'u miliyan uku a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.


Kwamitin ya bayyana hakan ne a jiya Litinin cikin wata sanarwa da Precious Elekima, Ko'odineta na Kudu-maso-Kudu kuma memba da ya fitar.


A cewar kwamitin, Rabi’u Kwankwaso zai yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su iya zabar shugabanni masu nagarta da kima.


Kwamitin na Kwankwaso ya kuma ƙaryata raɗe-raɗin cewa zai narke ya haɗe da na takarar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.


Kwamitin ya ce Atiku zai gwammace, "ya ruguje tsarinsa ya shiga tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na Sen. Kwakwanso a wani taron da aka shirya yi a ranar 22 ga Fabrairu, 2023, a otal din Transcorp Hilton.