Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zamanta a Kano, a yau Litinin ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta yi biyayya ga halin da ake ciki a da, na ayyana Muhuyi Magaji Rimingado da ta kora a matsayin shugaban hukumar yaki da cin-hanci da rashawa ta jihar, a Æ™arar da ya shigar har sai ta saurari korafe-korafen sa.  


'Status quo ante bellum 'yana nufin halin da ake ciki kamar yadda ya kasance kafin jayayya.


An shigar da karar a gaban mai shari’a E.D. Esele, inda gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar da kuma babban lauyan jihar Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 da na 2 da na 3.


Rimingado ya na kalubalantar sahihancin matakin da gwamnati ta dauka na korar shi ba tare da bin ka'ida ba.


A bisa wannan umarnin, wasikar korar da aka mika wa Mista Rimingado ba ta da wani tasiri, inda kuma hukuncin da kotun masana’antu ta kasa a Abuja ta yanke a baya ya na nan sai dai idan kotu ta yanke hukunci saÉ“anin wannan na baya.