A Cikin Wata Guda Na Samu Ribar Sama Da Naira Dubu 150,000, Inji Matashi Mai Kwalin Diploma Da Ya Rungume Sana'ar Sayar Da Aya Da Gyaɗa A Jami'ar Ɗanfodiyo
Usamatu Abdulƙadir Shehu ɗan asalin jahar Sakkwato, wanda ya kammala karatunsa na ƙaramar diploma a sashen nazarin aikin jarida dake kwalejin ƙere-ƙere ta Umaru Ali Shinkafi dake Sakkwato, a shekara 2022 da ta gabata, ya ce a cikin wata ɗaya ya samu ribar sama da 150,000 da sana'arsa ta sayar da Gyaɗa da Aya.
Usamatu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin PEN PRESS UDUS a harabar jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, ya ce mahaifinsa ne ya ba shi shawarar cewa kar ya zauna hannu-rabbana ba tare da yin wata sana'a ba; shi ya sa ya yanke shawarar rungumar wannan sana'ar domin rufa wa kansa asiri kamar yanda yake cewa:
"Mahaifina ya faɗa min cewa kar in zauna haka nan ba sana'a, daga nan sai ni yanke shawarar fara sayar da Aya da Gyaɗa kasancewar abubuwa ne da mutane kan ci a koyaushe," Usamatu ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa ya fara sana'ar ne tare da buga teburi a kusa da gidansu inda ya fara da sayo mudu 1-2 ya sayar cikin kwana 5 zuwa 6. Ya ce daga baya har ya soma ɗaukar sana'ar tasa zuwa kwalejin Umaru Ali Shinkafi da kuma jami'ar jahar Sakkwato, inda bayan waɗannan makarantun sun tafi hutu sai ya dawo a jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da sana'ar tasa kuma yanzu yakan sayo mudu 10 ya sayar cikin kwana biyu.
Usamatu ya ƙara da cewa yanzu kusan shekara ɗaya ke nan da ya fara wannan sana'ar amma a halin yanzu jarinsa ya fi ƙarfin 300,000.
"Cikin wata ɗaya na samu ribar sama da 150,000 kuma a halin yanzu na fi ƙarfin 300,000 da wannan sana'ar," in ji Usamatu Abdulƙadir.
Usamatu dai yakan zagaya ne ɗauke da soyayyar Aya da Gyaɗa a hannayensa yana sayarwa aji-aji a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, abinda ya ja hankalin jama'a musamman ma ɗalibai ganin cewa ga shi kyakkyawan matashi amma ya zaɓi ya rinƙa bi aji-aji yana tallata sana'arsa.
Daga ƙarshe ya kuma shawarce ƴan-uwansa matasa da su nemi sana'a komi ƙanƙantarta maimakon su zauna suna jiran aikin gwamnati domin shi kam sai hamdala saboda har kyauta wasu ƴan mata ke ba shi suna faɗin ya burge su.
0 Comments
Post a Comment