Mai Martaba Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garba Al Amin ElKanemi, ya bayyana irin taimakon da Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso yayi wa jihar Borno a matsayin abinda suke jinjina masa akoda yaushe kasancewarsa babban Dan siyasa.
Ya bayyana Hakan ne a wata Ziyarar girmamawa da Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ya Kai masa a fadarsa dake Maiduguri a ranar Talata.Shehun Borno ya yaba da yadda Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso yake gudanar da mulkinsa tare da zaiyano masa irin tarin matsalolin da suka addabi jihar Borno, Wanda suke rokon da idan Allah ya bashi Nasara yazo ya gyara musu.
Cikin sanyaya zuciya da furta kalamai masu ratsa zuciya Mai Martaba Shehun Borno yace "Mu Alummar jihar Borno Muna cikin Wani Hali, ka duba wadannan hakiman nawa yawancinsu sun baro yankinsu sun dawo cikin gari da zama, Kuma ba Wani abu bane ya Sanya haka illa Rashin tsaro da Kuma matsalar hanya, domin matsalar hanya itace take Kawo rashin tsaro, don haka your excellency munaso idan Allah ya baka Nasara a taimaka a gyara mana, domin a Maida mu yadda muke, jihar mu Mai kyau wadda kakanninmu suka kafa ta" inji Shehun Borno.
A nasa jawabin Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana garin cikinsa da yadda Mai Martaba ya tarbesu tare da bayyana cewar da zarar Allah ya bashi Nasara ba shakka Jihar Borno tana cikin jihohin da zasu fara Kawo gyara a cikinta.
0 Comments
Post a Comment