Wasu matsoratan 'yan siyasa a jihar Borno sun tura karnukan farautarsu suka farfasa billboard mai dauke da hoton 'dan takaran Shugaban Kasa a jam'iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da na dan takaran kujeran Sanatan Borno Central H.E Attom Magira
Manyan billboard ne kamar yadda zaku gani da aka kafesu a sassan gurare masu muhimmanci dake cikin birnin Maiduguri, amma yau an wayi gari duk an lalata su saboda tsoro da siyasa na rashin hankali
Lallai jagoran jami'ar NNPP a jihar Borno H.E ATTOM MAGIRA ya nuna jarunta wajan tallata jam'iyyar NNPP a jihar Borno, da alama farin jinin Kwankwasiyya ya tsorata Zulumiyya a Borno, a baya har ofishin NNPP aka rufe a birnin Maiduguri
Kuma babu shakka irin wannan mataki da suke dauka na ta'addanci babu abinda zai yiwa jam'iyyar NNPP a Borno sai karin karfin gwiwa, Sannan talaka a Borno zai kara fahimtar waye APC kuma su waye jagororinta, kuma talaka zai gane wadancan mutanen basu cancanta zu wakilceshi ba ko kuma su jagoranceshi
0 Comments
Post a Comment