Mai Martaba Sarkin Karshi Farfesa Sani Mohammad Karshi III, ya baiwa Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Sarautar Jarumin Karshi, bisa irin namijin kokarin da yake yi wajen riko da gaskiya da Amana.
Farfesa Sani yayi jawabi tare da nuna Jin dadinsa da yadda Sanata Kwankwaso yayo tattaki da sanyin Safiyar Nan domin yazo masarautarsu su gaisa.
A jawabinsa Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso yayi Godiya da wannan kyauta da aka basa tare da yin Alkawarin ci gaba da kula kyakkyawar alaka ga wannan masarauta.
A tare da tawagarsa akwai Mataimakinsa Bishop Isà ac Idahosa, Engr Buba Galadima, Dan takarar Gwamnan Jihar Nassarawa a Jamiyyar NNPP da mataimakinsa da dai sauransu.
#NasaraRadio
#AmanarTalaka
0 Comments
Post a Comment