A wannan rana ta Laraba 25/1/2023 Kansilolin karamar hukumar Rano guda biyar suka bayyana ficewarsu daga Jam'iyyar APC me Mulki suka Kuma koma cikin Jam'iyyar NNPP me kwandon kayan dadi..
Kansilolin sun bayyanawa Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum cewar matsin lamba da ake musu da Kuma Gaza yi musu ayyuka a mazabunsu da rashin karbar bukatun Al'ummar su ne wasu cikin dalilan fitarsu..
Kansilolin sune:
1-Kansilan Mazabar Rano Dawaki Kuma (Speaker) na Majalisar Kansilolin.
2-Kansilan Rurum tsohon Gari Kuma (Majority leader) na majalisar Kansilolin.
3- Kansilan Mazabar Rurum Sabon Gari (Former Speaker).
4-Kansilan Mazabar Yalwa.
5- Kansilan Mazabar Madaci..
Fatihu Yusuf Bichi
25/1/2023
0 Comments
Post a Comment