A Ranar 22 Ga Watan Augusta 1941 a Zamanin Yaƙin Duniya na Biyu : Sojojin Jamus sun fara mamayar Leningrad a Rasha .


Menene manufar kewaye birnin Leningrad?


Hit-ler ya daɗe yana ɗaukar mamaye Leningrad a matsayin babbar manufarsa ta kwashe Arziƙin kasar Rasha, saboda A kwai fiye da masana'anta 600 A cikin birnin Domin birnin shine na biyu a yawan masana’antu Bayan birni Moscow. 


Wanene ya ci nasara a Leningrad kuma me yasa?


A ranar 27 ga Janairu, 1944, sojojin Soviet sun karya layin kewaye na Leningrad na dindindin, wanda ya kawo karshen mamaye birnin na kusan kwanaki 900 da Jamus ta yi, wanda ya jawo asarar daruruwan dubban rayukan Rasha. Mamayar ta fara a hukumance a ranar 8 ga Satumba, 1941.