Daga Tukur Danmuazu
Duk cikin yan takara babu wanda yana kan wata kujera yayi amfani da ita wajen gatanta talaka, kare mutuncin talaka, renon talaka, kuma ya bata da masu karfi akan talaka kamar Kwankwaso.
A yau idan naga talaka na zagin kwankwaso, sai in fara jin tsoron yanuwana talakawa. A idon su ya daukaka talakawa da yayansu, ba wai tarihi ake basu ba, balle suce karya ne. Amma wai wasu talakawan su fito suna fadin baza su zabi kwankwaso ba harda su zargi, zagi da zambo.
In kace mene dalili? Wasu suce wai raayi. Raayi ko butulci? Wasu suce yayi sata. Idan akwai shedar satar da yayi, shin ta kai yawa da kazantar wanda kace zaka zaba? Wasu kuma sun rasa abinda zasu ce, sai suka fara cewa wai baida kunya, baya girmama nagaba tunda yana maganar da basa so akan yantakarar su. So kuke ya kira sunan su yace sallahu alaihim wasallam? A cikin tsofaffin da kuke so, waye ba tantirin daniska ba mare kunya mai rawa da karuwai a bainin jama'a? Sunfi magajiya barikanci, kuma sunfi biri barna.
Ba gardama na nema ba. Kuma banyi magana don ku fasa raayinku ba. So nake ku gane idan da amana ruwa bazai cinye kifi ba. Talaka dai, musamman na Arewa, wanda idan an kashe shi a kudu ba wani shugaban shi mai kai mishi dauki sai Kwankwaso bai kamata ya aibata Kwankwaso ba koda bazai zabe shi ba.
Ni dai a matsayina na takaka ina kaunar duk wanda ya nuna min kauna a aikace, ba surutu ba. Ko kuturu ne ban fasa kaunar sa. Abin da wasun ku basu gane ba shine masu kudi da yaran su basa kaunar kwankwaso. Suna da labarin abinda yayiwa mahandaman masu kudi yana gwamnan Kano. Ya kwace filayen da suka mamaye ya rabawa talakawa. Ya hana su amafani da kudin gwamnati suna ba yayansu scholarship zuwa kasar waje, ya kwasa yaba yayan talakawa tibis irina. Akwai wanda ko Zaria in zaizo sai dangi sunyi karo-karo zai sami kudin mota, amma sai ga irinsu a Turai da Asiya suna digirgirewa. An kone kasuwa da gidajen talakawa a Kudu, ya bar aikinsa na gwamna ya tafi, ya jajanta yayi gudummuwa kuma ya dawo ya dauki mataki. Idan masu kudi marasa gaskiyan cikinsu basa son Kwankwaso, kai danuwana talaka mene dalilin ka? So da gata da ya nunawa talakawa ne ya zama laifi kaima a wajenka? Koko kawai campaign ne na makiyan talakawa ya rude ka?
Ni ba dan jamiyyar Kwankwaso ba ne. Hakanan ni kwankwaso bai taimakeni a karan kai na ba, kuma ba danuwana ko guda daya na jini daya taba samun komai ta hannun kwankwaso. Amma talaka ne ni. Nayi imani cewa makiyin talaka a ko ina yake, makiyi na ne. Masoyin talaka a ko ina yake, masoyi na ne. Ban ganin masoyin talakawa a aikace kuma zahiri sannan ince ban son shi. Dan halas nake mai tarbiyar amana. Ban taba yi ba, kuma bazan yi ba har abada: butulci, in juyawa wanda yayi min aikin kauna baya. Allah ya kiyaye dan halas da aikin butulci.
Banda kuria don ban taba register ba saboda dalilan da suka shafe ni. Hanyar da zan nunawa Kwankwaso godiya akan abinda yayiwa yanuwa na talakawa ita ce, in fito fili in bayyana gaskiya kuma in fadakar. Nawa gudummuwar kenan. Kada Allah yasa muba masoyi kunya. Idan masoyi zai nasara muna tare; idan kuma faduwa ta same shi, ina nan mu fadi tare. Rayuwar kenan. Allah ya taimakawa talakwan Nigeria, ya bamu mafita.
0 Comments
Post a Comment