Kungiyar likitoci ta Najeriya ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wani likita mai suna Dakta Uyi IIuobe, wanda rahotonni suka ce 'yan uwan wani marar lafiya ne suka kashe shi a asibitin Oghara a jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Rahotonni sun ce mutanen sun kashe Illuobe ne ranar 31 ga watan Disamba, bayan da suka zarge shi da sakaci wajen mutuwar ɗan uwansu a asibitin.
A wata sanarwa da shugaban ƙaungiyar likitoci ta ƙasar Dakta Uche Ojinmah ya fitar ranar Litintin, ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar da ta yi dokar haramta cin zarafin ma'aikatan lafiya a ƙasar.
Mista Ojinma ya ce ''Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya ta kaɗu tare da bayyana baƙin cikinta game da labarin kisan Dakta Illuobe, da 'yan uwan wani marar lafiya suka yi a asibitin Oghara inda yake aiki''.
“Abu ne da ba za a lamunta ba cin zarafi tare da kisan ma'aikatan lafiya, likitan da ke cikin likitoci ƙalilan da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kula da lafiyar al'ummar ƙasa'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Muna kuma yin Allah wadai tare da kira ga gwamnatin jihar Delta da babban sifeton 'yan sanda na ƙasa, da su bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da mutanen da suka aikata wannan laifi domin su girbi abin da suka shuka''.
A makon da ya gabata ma dai hukumomin asibitin koyarwar Ilorin a jihar Kwara ta tsakiyar Najeriya sun ƙi bayar da gawar wani mutum da ya mutu tare da kama ɗaya daga cikin 'yan uwan mamacin bisa zargin lakaɗa wa wani likitan asibitin duka.
Rahotonni sun ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan uwan mamacin sun doki likitan a sashen kula da masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin.
0 Comments
Post a Comment