كتب عليكم القتال وهو كره لكم وعسى ان تكرهوا شيئا وهو خير لكم وعسى ان تحبوا شيئا وهو شر لكم والله يعلم وانتم لا تعلمون .}البقرة

   (An wajabta maku yaƙi , a halin ba kwa son shi, so da yawa kuna ƙin abu, a halin alkhairi ne a gare ku, kuma so da yawa za ku so abu, a halin sharri ne a gare ku, Allah ya san komai , amma ku ba abinda kuka sani). Baqara 216.


    Asiran da suka ƙunshi alkhairan da Allah TA'ALA yaɓoye a cikin wannan Gagarumin zalunci , suna da yawa ga kadan daga cikin su :- 

   1. Tsawan rayuwar Maulana Amirul-wa'izina yana ta shelanta wa Duniya akan wannan Jihadin da yake yi baya tsoran mutuwa... To zaafafan kalmomin da yagatsawa Alqali sun gasgata wancan Quduri na shehun malamin. 

   A kwai masu binsa domin Allah da suka ce wallahi da ya nemi afuwar alqali to da daga rannan sun rabu da shi.


   2.Badan zartar da wannan hukuncin da Kunzumin masu hankali suke ta yin wadarai da shi ba , da wasu daga tsirarun masu hankalin da suke ganin beken shehun malamin basu dawo daga rakiyar Kiyoshin sa ba. 


3. Ana ta gayawa Duniya :- Rayuwar Amirul-wa'izina suke ta nema ko ta halin ƙaƙa, ba wai hana shi karatu kawai ba..., Kamar da suka ɗauki rayuwar Liman Aliyyul-khawwasu rahimahullah... Amma mutane da yawa basa yarda, amma yanzu Gari ya waye... kowa ya san inda aka dosa . 


4. Wannan hukunci ya jawowa masoya Mal. Abdul-jabbar Hafizahullah ƙaffara wato Gafarar zunubai, ta hanyar shiga Damuwa da ƙunci da suka yi , wasu ma har shahada hakan tasabauta masu. 


5. Masu zaton jinin Shehun malamin wani ƙasƙantaccen jini ne, wanda Al'ummah bata damu da shi ba, sun tabbata sun tafka babban kuskure; Jinin shehun malamin ba laumar tuwo ce wadda za a hadiye ta cikin sauki ba. Bari wannan magana jinin Maulana Ayar Allah ce, ture kaga tsiya... Nan gani, nan bari, se ta Allah ta yi, !!!


   HASBUNALLAH WA NI'IMAL WAKIL !!!


قد كان ما خفت أن يكون + انا إلى الله راجعون 

    02 WASU DAGA NASARORIN BAYAN YANKE HUKUNCI GA MAULANA AMIRUL-WA'IZINA HAFIZAHULLAH 


    Yunƙurin maƙiya Mal. Abdul-jabbar akan kashe shi , ya tona ashirin su, ya ƙara jawo masu hasara me yawa :- 


* Ya tantance Magadan Banu-Hashim da magadan Banu-Umayya, Magadan Alawiyyawa da Magadan Mu'awiyawa, na wannan zamanin. Wallahil azeem duk inda kasamu kanka, ya nuna da a wancan zamanin kazo to anan za ka tsinci kanka.  


* Da yawa daga magoya bayan su sun yi masu bara'a.


*  Wasu Sun rasa Kujerun su na Halifanchi, wasu na aikin gwamnati, wasu Muƙamin su na siyasa, Wasu ma ran su suka rasa ta hanyar mutuwar bazata(Fuji'ah)... amma jama'a da yawa ko a jikin su, hasali ma tawile-tawile suke ta yi, sabo wanda aka yankawa kazar wahala wlh se ya fiye ta... 

من يهدالله فهوالمهتدي... 


* Wasu manya sun rasa Amincewar da yawa daga mabiyan su, dama Duniya baki daya.


*  Ya tabbatar da jahilcin wasu da ake zaton malamai ne, ko kuma tsantsar rashin tsoran-allansu da munafuncinsu da zalunci su da kwadayin abin-duniyar su.


*  Ya kara nunawa Duniya Lalacewar Nageriya da jahar Kano a wannan ƙarnin, musamman a bangaren sharia da Lalacewar kotuna... 


   Inna lillahi wa Inna lillahi raji'una !!!


Zawiyar Qadiriyyah Nasiriyyah Ung fari Karaye. 1/1/2923. Fi amanillah.