Hoto. 


Babban Masallacin Kano (Da Larabci : الجامع الكبير في كانو ) babban masallacin Juma'a ne a Kano babban birnin jihar Kano Masallacin na nan ne A cikin birnin Kusa Da Gidan Sarkin Kano, daura da yankin Mandawari a Birnin.


Babban masallacin Kano shi ne masallaci mafi tsufa a Najeriya Wanda Sariki Kano Muhammad Rumfa Ya Gina a karni na 15.


A lokacin An Ginashi Da Tubalin Laka, Kuma An Ginashi  Kamar Ginin Soro Da Husumiya, Sarkin Kano Muhammad Zaki ya Budeshi a Cikin Shekarar 1582, kuma Abdullahi Dan Dabo ya sake gina shi a tsakiyar karni na 19 


An Rushe shi a shekarun 1950, kuma an sake gina shi da tallafin Gwamnatin Mulkin mallaka ta Burtaniya.