Mataimakin dan takarar shugabancin Æ™asa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya bayyana cewa mai gidansa, Bola Tinubu, ya fi shi lafiya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Lahadi da daddare a wani shiri na kai-tsaye ta Facebook, mai taken "Fashin Baki", wanda Bulama Bukarti, Nasir Zango, Abba Hikima da Jaafar Jaafar su ke shirya wa.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, ana nuna damuwa kan yanayin lafiyar dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, inda wasu ke cewa bai cancanci zama shugaban kasa ba.
Amma Shettima ya ce Tinubu ya ma fi shi lafiya domin ba shi da ciwon suga ko hawan jini.
“Bari in fada muku karara cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mutum lafiya garau ya ke. A ajiye siyasa a gefe, Tinubu na da lafiya a jiki da kuma karfin tunani da zai iya rike Nijeriya.
“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fi ni koshin lafiya kasancewar ni ina da ciwon suga da hawan jini, wanda shi kuma ba shi da shi. Ko da ma cutar Parkinson da mutane suka yi magana game da ita, rashin barci ne kawai. Da zarar ya sami isasshen barci, zai zama ya yi garau.
“Shugabanci ba kamar aikin Æ™arfi na daukar buhunan siminti ba ne. Yawanci aiki da Æ™waÆ™walwa ya fi yawa a kan da jiki. Tsofaffin shugabannin kasa, Theodore Roosevelt da Abdelaziz Bouteflika da Daniel arap Moi na Amurka da Aljeriya da Kenya sun jagoranci kasashensu ta hanyar bunkasar tattalin arziki yayin da suke kan keken guragu," in ji Shettima.
0 Comments
Post a Comment