mutanen kabilar North sentinel Island. Kabilar da tafi kowacce ban tsoro da kuma kebewa daga cikin al’umma.


A zanen taswira, North sentinel Island yana yanayi ne da sauran gurare na indian Ocean wanda yake kewaye da kwawar teku masu daukar hankali. North Sentinel Island yana nan ne a bakin tekun Bengal dake Andaman archipelago.


Shi dai North Sentinel Island ba kamar sauran gurare na bakin ruwa bane da aka sani domin kuwa a kan kwatanta ko misalta shi da waje mafi wahala mafi muni sannan kuma wajen da ya fi ko wane waje tsoro yayin ziyara, sannan kuma guda ne ga mutanen da suka fi kowannen mutane kadaita ko kuma ware kansu daga sauran mutanen duniya.


Wannan abu na abin mamaki da ake dangata wadannan mutane da shi ba zai iya misaltuwa ko aunawa a ma’auni ba kai tsaye, amma mafi yawan gaskiyar ita ce, a kiyasi na kamar shekara 60,000 North Sentinel Island ya kasance gida ne ga kabila masu cin gashin kansu kuma suke ki' suna hana sauran  mutanen duniya kusantar su karfi da yaji.


Idan aka hango North Sentinel Island daga sama kamar yadda tauraron dan’Adam na European Space Agency ta labarta.


Kabilar “Sentineli” sun kai hari ga kusan duk wani mahaluki da ya shiga yankinsu. a shekarar 1896 sun soki wani dan Indiya wanda ya gudo daga birninsu har ya kasance cewa ruwa ya kawo shi zuwa bakin gabar ruwan da suke har lahira, a shekara ta 1974, sun yi wa wadansu ‘yan daukar fim ruwan masu, (kwari da baka) shekara ta  2004 kuwa daya daga cikin mutanen kabilar ne ya saita sannan ya harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu wanda yake shawagi a sararin Subhaana sakamakon tura shi da aka yi ya duba ko akwai wadanda suke a raye har zuwa lokacin' bayan an sami yanayi na girgizar kasa, a baya bayannan ma a shekarar 2006 mutanen sun kashe wasu masu ‘su’( masu kamun kifi) wadanda suka fada kogin yankinsu bisa kuskure


Tsuguno dai bata kare ba, domin kuwa bayan an tura jirgin sama mai saukar ungulu akan ya je ya taho da gawarwakin wadanda suka kashe din kuwa, mutanen sun sake kai hari ne wa shi kansa jirgin.


Wannan muguwar dabi’a ta mutanen North Sentinel Island ne ya sanya aka kasa sanin wani abu mai yawa game da wannan kabila, abin da aka sani kawai shi ne suna da makamai musamman irin danginsu kwari da baka, sannan kuma suna amfani da raga irin ta kamun kifi, suna amfani da kwale-kwale, su kan yi kamun kifi, su shiga daji domin samun ganyayyaki na daji, amma babu wani labari na noma ko kiwo ko kuma wani abu da ya danganta su da kunna wuta ko da kuwa irin ta ita ce ce, mutane su kan yada jita- jitar cewa mutanen Sentinel su kan jira ne har sai an yi tsawa sannan kafin ta hura musu wuta a jikin gunguma-gunguman itatuwan da suka hada wanda za su yi ta amfani da shi har na tsawon wani lokaci.


Sanannen abu ne cewar kabilar sentinel su ne mutane na karshe dake rayuwa a duniyar nan wanda ya kasance cewar ba wanda yake taba su ko kuma zuwa kusa da su da abin da ya danganci zamani.


mutane sun yi kokarin bincike akan kabilar sentinel inda wasu suka yi nasarar samun wadansu bayanai kalilan.


A shekarar 1771 wani mai binciken yanayi na kasar Birtaniya mai suna John Ritchie ya wuce ta wannan waje, ya ce daga bangaren Kudu maso Yammacin Andaman akwai gabar wani kogi mai kyau wanda yake rufe da bishiyoyi yana da girma da tsawo sannan kuma idan za mu yanke hukunci daga yawan hàske da ake iya hanga daga wajen za mu iya cewa wuri ne da ya dace da rayuwa, 'jirgin na ruwa ya yi ta shawagi har tsawon wasu shekaru yana kewayawa yana komawa har na tsawon shekara 100, amma ba’a sami wani abu na dorar wa game da mutanen ba.


A shekarar 1869 jeremiah Homfray, mutumin da ke da alhakin kula da Andamanese ya yi tafiya zuwa Sentinel Island domin binciko wadansu masu laifi wadanda suka kubuta daga penal Colony a Port Blair.


Da fara isarsu, Homray wanda yake tafe da rakiyar ‘yan sanda da da kuma wadansu daga cikin Andamanese suka hango wadansu mutane su goma zaune a bakin tekun ‘tsirara ’suna da dogon gashi rike da ‘kwari da baka’ suna harbin kifi.


Daga nan dai mutanen na Sentinel suka nemi waje suka boye bayan sun hango wannan jirgi na su Homray. Mutanen na Andamanese da suka kasance cikin firgici tsoro da kuma faduwar gaba yayin da suka hango abin da ke faruwa, sun gargadi Homfray da kakkausar muraya a kan hatsarin da ke tattare da wadannan mutane, amma sai ya yi bitis da gargadin na su ya kuma sanya wa ransa cewar ya isa wannan waje inda kuma hari ne ya biyo baya daga wadannan mutane.


A wannan shekarar kuma wata tawaga ta ‘yan kasuwa daga indiya sun fado wannan waje sakamakon jirginsu na kasuwanci da ya farfashe a cikin kogi har ya wanko su zuwa North Sentinel bayani ya nuna cewa mutane 86 daga cikin wadanda suka rayu cikin fasinjan jirgin da kuma mutum 20 daga cikin masu kula da jirgin sun sauka lafiya a bakin tekun.


A kwana na uku da saukarsu ne kuwa ‘yan kabilar Sentinel suka kawo masu hari. Kyaftin din jirgin ya ce: mutanen suna zamane a tube ma’ana tsirara, suna da guntun gashi da kuma hanci ja, sannan suna bude bakunansu domin fitar da wata irin kara kamar na namun daji, suna amfani da baka wanda sukan yi tsinin bakinsa da karfe, kyaftin din ya ce ya kubuta ne daga hari wadan nan mutane ta kan burbushi jirgin yayin da kuma aka kawo masa agaji kwanaki da dama bayan ya kubuta ta hanyar wasu matafiya da hanya ta wuto da su ta wajejen inda daga baya kuma aka tura jirgin ruwa irin na yaki domin ceton sauran wadanda suka rayu wanda suka samu suka gudu daga tekun Sentinel da taimakon duwatsu da itatuwa.


Bayan wannan ruguntsimi kuwa, an share sama da shekaru goma 13 ba tare da wani ya sake waiwayar wadannan mutanen ba.


A Janairu na shekarar 1880 ne kuma wasu mayakan Britaniya suka sami nasarar sauka a tsibirin na North Sentinel, mayakan, karkashin jagorancin Maurice Bidal Portman dan shekaru 20 sun shiga tsibitin neman wadan nan kabila inda suka suka ci karo da hanyoyi ma banbanta da kuma sababbin kauyuka wadanda aka yi watsi da su.


Portman ya ce yanayin girki da sarrafa abinci na mutanen Sentinel ya yi kama da na mutanen Onges, ba irin na aborigin da mutanen Andaman ba. A lokacin wannan zagaye Portman ya ce bai gamu da ko mutum kwaya daya ba na daga wannan kabila duk sun watse cikin daji.


Cikin sa’a ne bayan wasu kwanaki masu dama ana bincike sai kuwa suka ci karo da mutum shida daga cikin Kabilar Sentinel wadanda suka kunshi mata da miji dattijai da suka manyanta sai kuma ‘ya’yansu guda hudu inda suka kama su, suka tattarasu suka mai da su Port Blair.