WANDA YA SAN DARAJAR GORO...
Wataƙila na san kun saba jin labarin mutanen da ke kashewa karnukansu maƙudan kuɗi don kula da su ko?
To sai dai, a wannan karon wata mata mai suna Meggy Johnson, ce ke kashe wa wasu tantabarunta biyu £4,000, kwatankwacin Naira Miliyan biyu da dubu É—ari biyu da motsi wajen kula da su, da kuma É—anÉ—asa musu kwalliya ta kece raini, abun gwanin ban sha’awa.
Da farko ta tsinci tantabarun ne a wani waje da aka yasar da su cikin wahala, ta kai su gida ta riƙa kula da su har tsawon makwanni shida, lokacin ne ta saba da su ta ƙaunace su, suka shiga ranta kamar me.
Budurwar mai shekara 23 da ke zaune a Lincolnshire, ta ce ta keɓe musu ɗakinsu musamman, ta ɗinka musu kaya kala kala, sannan takan je kanti don yi musu siyayya, kuma kowaccensu na da kayan da yawansu bai gaza kala 17 ba aƙalla.
Ana shirya musu ƙayataccen bikin murnar ranar haihuwarsu har ma a yanka musu Kyak.
Dama dai Hausawa kan ce wanda ya san darajar goro shi yake yafa masa algarara.
Daga Taskar Nasaba
0 Comments
Post a Comment