Yanzu na ci karo da wata sanarwa daga Gwamnatin Kano. Sanarwar, wacce ta fito daga Kwamishinan Yada Labarai na Jiha Kano Mal. Muhammad Garba, ta bayyana cewa wai Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam'iyyar NNPP Engr. Abba Kabir Yusuf ya na yunkurin rusa Masarautun Jihar Kano idan Allah Ya bashi nasara a babban Zabe mai zuwa.
Amma abun tambaya shi ne: a ina Abba Kabir ya yi wannan ikirari da su ka ce ya yi? Hirar dai da su Audu Bulama Bukarti su ka yi da shi, babu inda Abba ya ce zai rushe Masarautu. Duk wanda ya saurari hirar da kunnen basira da kuma budaddiyar zuciya, zai tabbatar da hakan.
A cikin hirar, Abba ya amsa tambayoyi a kan batutuwa da yawa. Cikin su kuwa har da yanda harkar Ilimi ta tabarbare a Jihar Kano a karkashin wannan Gwamnati; da maganar Faifen Dollar; da cefanar da kadarorin Gwamnati kamar Makarantu da Badala da sauran gine-gine da filaye ba bisa ka'ida ba; da batun 'Yancin Kananan Hukumomi; da shigo da Iyali dumu-dumu cikin harkokin Gwamnati da sauran batutuwa. Mai ya sa Gwamnati ba ta mayar da martani a kan daya daga cikin wadannan ba, sai maganar Masarautu?
Ya kamata Gwamnati ta mayar da hankali wajen yi wa jama'ar Jihar Kano bayani a kan wadannan muhimman al'amura wadanda kai-tsaye su ka shafi tattallin arziki da walwalar su, maimakon yada farfaganda maras tushe. Jama'ar Jihar Kano dai masu ilimi ne da fahimta, a dena kokarin yin wasa da hankulan su. Karrrr su ke kallon kowa!
Bashir I. Kabo,
Janairu, 2023.
0 Comments
Post a Comment