fitaccen malamin addinin musuluncin Marigayi  Sheikh Jaafar Mahmud Adam, ya kasance mutun mai son cigaban yankin Arewa mai tsananin kishin musulunci da musulmai wanda ba zai taba goyon bayan burin jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasar Najeriya ba.


A wata huɗuba mai fashewa kafin a ka*she shi a shekarar 2007, Sheikh jafar mahmud Adam ya sanya Bola Tinubu a cikin jerin makiyin Arewa daga Kudu maso Yammacin Najeriya. 


A lokacin da yake gwamnan Lagos an ka*she mana yan uwa da yawa a jiharsa yakasa daukan mataki an mana asaran dukiya mai dumbin yawa a jihar Lagos


Haka zalika Bola Tinubu ya jagoranci ƙona kimanin babura sama da dubu 3,500 tare da fatattakar ƴan Arewa daga kasuwar Alaba rago wanda a lokacin yana Gwamnan Lagos ko mai yankan akaifa aka gani indai Ɗan Arewa ne sai an karbi kuɗi daga wurin shi don kawai a musgunawa ƴan Arewa.