Rikicin PDP a Kano: Tsagin Sagagi ya yi watsi da kafa kwamitin kamfen da Shekarau ya yi
Wani tsagi a jam’iyyar PDP a Kano, karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi, ya yi watsi da kafa wa da kuma kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar a zaben 2023.
A ranar 5 ga watan Janairu ne dattawan jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, su ka ƙaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyya, karkashin jagorancin Yunusa Dangwani a Meenah Event Center a babban birnin jihar.
Da yake mayar da martani kan kaddamarwar, lauyan PDP na ɓangaren Sagagi, Isa Wangida, ya bayyana matakin a matsayin raini ga kotu.
"Mun lura da abin takaici da rashin bin doka da oda da aka yi na bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar PDP na jihar Kano karkashin jagorancin kwamitin riko," Wangida ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi.
Wangida ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar na jihar, karkashin jagorancin Sagagi sun ɗaukaka kara da kuma dakatar da kaddamar da kwamitin, wanda hakan ya basu damar ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki.
Wangida ya kara da cewa matakin na dattawan jam’iyyar ya kuma saba wa umarnin kotu da mai shari’a A.M Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar, inda ya bayyana Mohammed Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.
Ya kuma ja hankalin ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar da cewa, “wadannan ‘yan adawar PDP a jihar Kano su ne ke ikirarin cewa mu ba shugabanni ba ne bayan hukuncin kotun daukaka kara da ta yi watsi da hukuncin da na Babbar Kotun Tarayya a Abuja.
0 Comments
Post a Comment