Tawagar malaman addinin Musulunci a Nijeriya, karkashin jagorancin Gambo Barnawa, sun yi ta’aziyya ga mabiya addinin Kirista a fadin duniya bisa rasuwar Paparoma Emeritus Benefict na 16 a ranar 31 ga watan Disamba, 2022 yana da shekaru 95 a duniya.


Malaman sun mika ta’aziyyar su ne a lokacin da su ka kai ziyarar sabuwar shekara ga Fasto Yohanna Buru, Janar Overseer Cocin Christ Angelical and Life intervention Ministry, Sabon Tasha, Kaduna.


Barnawa ya ce sun ziyarci gidan Buru ne domin taya shi murnar shiga sabuwar shekara, inda suka yi amfani da damar wajen mika sakon ta’aziyyarsu ga mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya bisa rasuwar Paparoma Benedict na 16.


Ya ce Paparoma mutum ne mai daraja, tawali'u, kuma mai kirki.


Ya ce Paparoma mutum ne mai son zaman lafiya da hadin kai, wanda hakan ya sa ya zama na musamman.


“Ya kwashe rayuwarsa yana addu’a da wa’azin zaman lafiya a duk faÉ—in duniya tare da haÉ“aka juriya da yafiya ga dukan É—an adam, ba tare da la’akari da Æ™abila, al’adu da addini ba.


"Duniya ba za ta manta da gudunmawar da Paparoma Benedict na 16 ya bayar na wa'azin zaman lafiya, soyayya, hakuri da kuma gafara a tsakanin dukkan bil'adama.