Kungiyar likitocin Nijeriya, NMA, reshen jihar Kwara, ta ce kusan ko wanne mako sai an samu hare-hare na jiki ko na baki a kan mambobinta.
Dakta Ola Ahmed, Shugaban NMA na jihar ne ya bayyana haka ga manema labarai a yau Litinin a Ilorin.
Ahmed ya koka da yadda ma'aikatan kiwon lafiya a cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a fadin jihar da kuma asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin, UITH, ke fama da duka da zagi ba gaira ba dalili.
“An samu labarin hare-haren da ake kaiwa mambobin mu a asibitoci daban-daban a jihar.
"An rubuta rahotanni da dama, gami da wasiƙu ga ma'aikatanmu, musamman ma hukumomin UITH da kuma Gwamnatin Kwara, amma ba mu ga wani gagarumin ci gaba ba," in ji shi.
Ahmed ya bayyana cewa hare-haren da ake kaiwa mambobin ƙungiyar akai-akai ya haifar musu da fargaba da razani na yayin da suke tsoron rayukansu.
Ya ba da misali da harin da wasu ‘yan uwan wani majinyaci da ya rasu suka kai wa wani memba na kungiyar Likitocin Resident Doctors, ARD-UITH kwanan nan.
Ya kuma yi tir da zargin kisan wani likita da dan uwan mara lafiya ya yi a Delta a yayin da yake gudanar da ayyuka, ya kara da cewa NMA ta Kwara ba za ta bari sai hakan ya sake faruwa a jihar ba.
0 Comments
Post a Comment