Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da mataimakinsa dan takarar shugaban kasa Bishop Isaac Idahosa sun kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP wanda ya gudana a Abuja.
A jawabinsa na bude taron, Sanata Kwankwaso ya bukaci daukacin ‘yan majalisar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa. Ya godewa dukkan abokansa da suke aiki a bayan fage domin shirya taron tara kudade ga jam’iyyar tare da godewa daukacin ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suke bayarwa.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP shine shugaban kwamitin sannan Folashade E. Aliu zata kasance sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar PCC ta kasa.
📷Saifullahi Hassan
0 Comments
Post a Comment