Ikon Allah!
Wai ni Abba Hikima Fagge, ni da nake fashin bakin hakkin dan adam, ni yan siyasa sukewa kashedin cewa na daina shiga harkokin siyasa. Saboda bani da hakki. So suke jama’a su dawwama cikin zalunci. Mu kuma mu dawwama gwamarmayar neman gyara aika-aikar su a kotu. Kullum muyi ta babatu sai kace mara sa aikin yi. To ba zai yiwu ba.
Bayan soshiyal midiya har radiyo sai na shiga na fadi ra’ayi na akan wadanda muke wa zaton alkhairi da dalilan mu a ko wace jamiyya suke. Kuma sai mun ja hankalin mutane akan abunda muka yadda dai-dai ne in sha Allah. Sanda na
daina wannan to bana numfashi.
Kuma tun yanzu ma ko ban fada kun sani. BANA RA’AYIN GAWUNA DA GARO. Kowa hakan zai bata wa ban damu ba. Yanci na ne kuma ba a makance nake ba. Badan komai ba sai don basu ga matsalar da mulkin Ganduje ya jawo mana a Kano yanzu ba.
Gawuna dai yayi rantsuwa da Allah yace amanar Ganduje zai rike. Kuma mun yadda da rantsuwar sa. Kuma ya fada, irin mulkin da Ganduje yake so shi zai yi. Shima Gandujen ya fada cewa halin su daya da Gawuna. Duk badakalar da ake yi yanzu Gawuna yace bai gani ba. Har EFCC dan matar gwamna ya kai maman sa. Kowa yaji labarin.
Ni kuma ban taba shan wahalar mutane ba irin wannan lokaci. Ban kuma san abubuwa sun taba tabarbarewa a Kano ba kamar yanzu. Kuma burin mu shine a samu wanda zai gyara.
Ni nasan irin tiri-tirin da nake yi da taimakon Allah akan al’amuran talakawa akan zakunci da karya dokar gwamnati kala kala a wannan gari.
Kuma in sha Allah sai na yi duk mai yiwuwa wajen chanja wannan tsarin da hannuna, da baki na da zuciya ta.
Saboda a halin yanzu ko shugabancin Nigeria bai dame ni ba kamar na Kano.
0 Comments
Post a Comment