Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN ya ruwaito cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, IBB, ya tafi kasar Jamus domin duba lafiyarsa.


Mahmud Abdullahi, mai taimaka wa IBB kan kafafen yada labarai kuma É—an uwa gare shi ne ya bayyana hakan ga NAN a Minna.


Abdullahi ya shaida wa NAN cewa, “Ban tattauna da Oga ba kafin ya bar Najeriya da inda ya je da kuma dalilin da ya sa.


“Na san ya kamata ya je a duba lafiyarsa domin ya dau tsawon lokaci bai je ba.


"Saboda haka na yi imani cewa ya tafi Jamus ne ranar Asabar don duba lafiyarsa."


Ya ce ba zai iya yin karin bayani kan tafiyar ba tunda bai tattauna da maigidan na sa ba kafin ya bar kasar.


Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa babu wani abin fargaba domin tsohon shugaban ya yi tafiya ne don duba lafiyarsa na yau da kullum.