Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin makon da ya gabata, ya ce kamfanin ƙera ƙarafa na Ajaokuta zai samar da ayyukan yi da aka kiyasta kimanin 500,000 ga matasan Nijeriya.


Shugaban ya bayyana haka ne a ziyarar kwana ɗaya da ya kai jihar Kogi a ranar Alhamis.


Ya kuma yi magana game da kudurin gwamnatinsa na mayar da Kogi a matsayin cibiyar masana’antu da kuma kafa cibiyar samar da makamashi da ma’adinai.


Ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta samu nasarar kawar da duk wani cikas ga ci gaban rukunin karafa na Ajaokuta.


A cewar sa, aikin ya kasance don amfanin al’ummar jihar sosai.