Dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar ADP, Sha'aban Ibrahim Sharaɗa, ya kalubalanci dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, bisa yadda yake nuna cewa ya yarda da Allah da kuma ikon Allah, yana mai cewa, idan har ya yarda da Allah, da bazai je ya yaga sakamakon zaɓe a shekarar 2019. 


Sha'aban wanda yanzu haka dan majalisar tarayya ne dake wakiltar karamar hukumar Birni, ya bayyana haka ne yayin taron bayyana manufofi na yan takarar gwamnan Kano da gidan Mambayya ya shirya a ranakun Asabar da Lahadi, inda yace abinda Gawuna ke fada ba shi yake aikatawa ba. 


Jawabin hakan na zuwa ne bayan Gawuna ya bayyana cewa ya kamata duk yan takara su yarda da Allah, domin shi dai ya yarda dashi, kuma rokon idan babu alheri a abinda yake nema, kada Allah ya bashi. 


A shekarar 2019 ne Gawuna tare da abokin takararsa, Murtala Sule Garo, suka je ofishin hukumar zaɓe INEC na karamar hukumar Nasarawa, tare da yaga sakamakon zaɓen mazabar Gama, abinda ya janyo sake maimaita zaɓe a wasu wuraren, musamman mazabar Gama, kamar yadda Rahotanni suka bayyana.