Bismillah wassalatu wassalamu Ala rasulillahi wa alihi aɗɗayyibina aɗɗabirina. Bayan haka ƴan uwa masu karatu ku biyoni cikin wannan rubutun domin warware muku shubuhar da malaman izala da wasu ƴan ɗariqa ke haɗawa aka cewa malam Abduljabbar yana yaɗa zagin annabi s.a.w, kamar yadda wasu ke faɗa, ko kuma yana zagin annabi saw kamar yadda wasu suke faɗa.


JAN HANKALI !!


Ɗan uwa mai karatu ka sani wannan maganar, maganar banza ce, babu wata magana komai muninta da bai halatta ka hikayantota ba, saboda duk wanda ya karanta al'qur'ani da hadisai da waqi'i yasan wannan qarya ce, ba gaskiya ba ne.


MISALAI.


Alqur'ani mai girma cike yake da miyagun kalaman mushrikai, yahudu da nasara da suka faɗa akan Allah SWT da manzon Allah saw. 


A cikin al'qur'ani, Allah SWT  ya hikayanto kalaman manyan kafirai, kamar fir'auna domin warware maganarsa da yimasa raddi.


KALAMAN ƁATANCI A JANIBIN ALLAH CIKIN AL'QUR'ANI.


1-Fir'auna yace shine Allah maɗaukaki.

2-Yahudu da nasara sunce Allah ya nada ɗa.

3- Yahudawa sunce uzairu dan Allah ne.

4- Nasara sunce masihu isah dan Allah ne.

5- Yahudu da nasara sunce mala'iku ɗiyan Allah ne.

5- Yahudu da nasara sunce Allah talaka ne.

6- Yahudu da nasara sunce Hannun Allah jimqe yake 

7- Kafiran makka sunce alqur'ani labaran tatsuniyoyi ne kawai 


KALAMAN ƁATANCI A JANIBIN ANNABI S.A.W CIKIN ALQUR'ANI.


1- Kafiran makka sunce Manzon Allah saw Mahaukaci ne.

2- Kafiran Makka sunce manzon Allah saw mawaqi ne.

3- Kafiran Makka sunce manzon Allah saw tatsuniyoyi ne yake karantawa.

4- Kafiran sunce manzon Allah masihirci ne.

5- Kafiran Makka sunce manzon wanda aka sihirce ne.


Waɗannan kaɗan daga cikin zage-zagen da Allah ya kawo cikin littafensa wanda akayi masa akawa annabinsa, domin ya karantar damu yadda zamu warware waɗannan ababen.


HUKUNCIN HAKAITO ZAGIN MANZON ALLAH.


Waɗannan malaman da suka qullama malam Abduljabbar sharri cewa yana zagin manzon Allah saw, daga qarshe suka fake da cewa abinda yasa, ba zasu zauna dashi ba, wai saboda munin kalamansa da yake faɗa kuma bai halatta a saurare shi ba. 


( Ka da ku manta sune da suka juye zagin da yake kawo yana raddi zuwa cewa shine mai zagin)


Dan uwa mai karatu, wannan maganar maganar banza ce, ta wawanci da hatta jahilin cikin gari yasan qarya ce zalla, saboda al'qur'ani ya bamu labaran zage-zagen da akawa Allah da Manzonsa, sannan bayan haka ya gaya muna yadda aka zauna, aka tattauna aka fafata tsakanin annabawa da masu kiran kansu Allah da masu zagin Allah, kuma annabawan sun sauraresu domin jin hujjarsu.


Wannan ka ɗai ya isa ka gane cewa wadannan mutanen maha'inta ne, Maqaryata, fasiqai, zindiqai da suka maida mutuncin manzon Allah matsayin shagon kasuwanci su.


Amma ga abinda malamai suka faɗa akan hukuncin HAKAITO ZAGIN MANZON ALLAH.


Shehu alqadiy iyadd ya kawo cikin littafensa na " kitabub shifa'i" juzu'i na 2 shafi na 249 fasali na takwas. Yace 


حكم الحاكي لهذا الكلام وغيره"

Hukuncin mai hikayanto wannan maganar (zagin annabi) da waninsa.


الوجه السادس : أن يقول القائل ذالك حاكيا عن غيره وآثرا له عن سواه'

Fuska ta shida. Itace mai faɗa ya fadi wannan zagin da akawa annabi alhali yana hikayanto shi daga waninsa, yana ruwaito shi daga waninsa.

فهذا ينظر فى صورة حكايته وقرينة حاله

Wannan, ana dubi cikin surar yadda yake HAKAITO maganar da qarinar halinsa. (Shin farin ciki ya ke yi lokacin bada labarin zagin da a kayi ko da damuwarsa yake nunawa )


ويختلف الحكم بإختلاف ذالك على أربعة وجوه"

Hukuncin HAKAITO ZAGIN MANZON yana saɓawa da saɓanin wannan, cikin fuska hudu.


Ga fuskokin

1-الوجوب

2-الندب

3-الكراهة

4- التحريم 

1- Wajabcin

2- Mustahabbanci

3- Karhanci

4- Haramcin.


(Ma'ana akwai inda wajibi ne ka kawo zagin da akawa annabi saw. Akwai inda mustahabbi ne ka fadi zagin, akwai inda anqi ka fadi maganar, akwai inda haramun ne ka HAKAITO ZAGIN)


فإن كان أخبر به على وجه الشهادة والتعريف بقائله والإنكار عليه وإعلام بقوله والتنفير منه والتجريح له، فهذا مما ينبغي إمتثاله ويحمد فاعله"

Idon ya labarta zagin da akawa annabi saw bisa ga fuskar kawo shaidu ( kamar kotu aka kiraka kayi shedar wane ya zagi annabi) da sanarwar mutane wanda yayi zagin, da yin musu gareshi, da bayyanar da maganarsa, da nisantar da mutane daga maganarsa da sukar wanda yayi zagin, wannan yana cikin abinda ya wajaba ko ya kamata ayi, sannan ana godema wanda yayi haka.


Na ce " Kunji abinda alqadi yace indai an kawo zagin domin faɗakar da mutane ne, da nuna musu kuskuren mai zagin da bayyana ɓarnarsa wannan yin hakan wajibi ne.


Alqadi iyadd ya cigaba da cewa 👇


وكذالك إن حكاه فى كتاب أو فى مجلس على طريق الرد له والنقض على قائله والفتيا بما يلزمه وهذا منه ما يحب ومنه ما يستحب بحسب حالات الحاكي والمحكي عنه"

HAKAMA IDON YA HAKAITO ZAGIN MANZON ALLAH DAKE RUBUCE CIKIN LITTAFI, KO A WURIN MAJALISI DOMIN YIN RADDI GA WANDA YA FADI MAGANAR, DA WARWARE MAGANAR AKAN WANDA YA FAƊETA, KO YIN FATAWA GA ABINDA YA LAZIMCE SHI, WANNAN DAGA CIKINSA AKWAI IN DA DOLE NE, A KAWO MAGANAR A WARWARETA, AKWAI WANDA MUSTAHABBI NE YIN HAKA, GWARGWADON HALI DA YANAYIN MAI HAKAITO MAGANAR DA WANDA AKA HAKAITO MAGANAR DAGA GARESA.


Wannan shine abinda alqadi iyadd ya faɗa akan hukuncin kawo ko maimata zagin da wani yawa annabi saw kazo kana faɗar zagin domin wadannan ababen da ya faɗa.


RUFEWA


Ƴan uwa ! Yanzu kun tabbata abinda mu keyi na kare martabar manzon Allah daga hadisan qarya da aka rubuta aka inganta cikin littafai wajibi ne akanmu sauke wannan nauyin, domin faɗakar da al'ummar manzo Allah saw abinda ke cike cikin littafai na sauke da naqqasa martabar manzon Allah s.a.w


Alqadiy iyadd ya tabbatar muna cewa indai maganar tana rubuce cikin litattafe dole ne a fito da ita a fadama al-umma muninta da kuskuren wanda ya fadeta domin su gujeta.


GA MISALAN IRIN WANNAN ZAGIN MANZON ALLAH DAKE RUBUCE CIKIN LITTAFAI.


1- hadisin Bukhari da Muslim cewa Manzon Allah saw ya faɗi tsirara cikin dubban dubatun al-umma wurin ginin ɗakin Ka'aba.


Lambar hadisi Bukhari Kitabus-swalati 364.


2- Hadisin Bukhari da Muslim : Annabi na shiga gidan matar aure tana shafa kansa ya kwanta kan gadonta gaf da ita tana shafar kansa har yayi bacci tana cire masa kwarkwata.


Lambar hadisi Bukhari 2788- 2789. Muslim lamba ta 1912.


3- Hadisin Bukhari da Muslim annabi yana halartar wuraren kiɗe-kide da raye-raye tareda shaiɗanun Mutane da Aljannu.


Bukhari lamba 5190.


4- Hadisin Bukhari da Muslim : Matan Manzon Allah sunce yaji tsoron yayi musu adalci saboda baya yimusu adalci ya karkata akan Nana A'isha har da umurtarta suyi zage-zage.


Bukhari lamba ta 2581. Muslim lamba ta 2442.


5- Hadisin bukhari da muslim annabi Saw yana zage-zage yana zaluntar mutane bisa kuskure.


6- Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana umurtar sashen matansa akan sashe su yi zage-zage ba.

صحيح البخاري 2581" مسلم 2442


7- Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana fitsari a tsaye kan hanya cikin bola ba.

البخاري 224" مسلم 273

 

8- Hadisin da ke cewa wai iyayen Manzon Allah da Baffansa wai 'yan wuta ne ba. 

مسلم "203"


9+ Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya aika wasu Sahabbai sun yi wa wani mutum wai da ke zaginsa kisan gilla cikin duhun dare ba. أخرجه البخاري (3032)، ومسلم (1801


7. Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW yasa an yiwa sama da mutum ɗari uku yankan raguna ba, a Banu Ƙuraiza bayan an duba gabansu an ga gashin mararsu ya tsiro.

 تخريج مشكاة المصابيح 3901 إسناده صحيح


8. Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW yana zaune tare da Sahabbansa wai ya kalli wata mace da za ta wuce wai a nan take  sha'awarsa ta motsa har ya tashi da sauri ya shiga gidansa ya je wa wata a cikin iyalinsa, wai kuma da ya fito ya gaya wa sahabbansa cewa  kaza da kaza na aikata.

صحيح مسلم  1404


9.Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW Yana zagayar matansa goma sha ɗaya cikin awa ɗaya da wanka ɗaya da rana haka da dare ya aikata haka ba.

 البخاري 5215


10.Hadisin da ke cewa an aiko ni domin in yanka ku ba.

صحيح الموارد : 1404


11. Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai yana cewa an sanya arzikinsa karkashin inuwar mashinsa ba.

تخريج مشكلة الفقر : 24


12- Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW yake cewa ba: wai an sa min son mata ba.

النسائي 3939 

Ibnu Hajar a Fat'hul Baariy 15/3 ya inganta shi!


13- Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya umurci ɗaya daga cikin matansa ta shayar da wani yaro baligi nononta ba.

البخاري 4000. مسلم 1453


14- Hadisin da ke cewa Annabin Rahama SAW wai ya halatta jinin wata mace mai ciki da wani makaho ya yi wa kisan gilla cikin dare ba..

أبو داود 4361.


Da ire irensu duka ban yarda da su ba! In kuma yarda da su shi ne SUNNAH, to gaskiya bana yin wannan kalar Sunnar!!


Jama'ar Annabi, waɗannan kaɗan me daga cikin Hadisan da Malam Abduljabbar yake faɗa dasu, yake qaryatawa domin kare Annabi SAW Amma maqiya Allah maqaryata suka juya zancen cewa shine yake fadar haka, shine ke taɓa janabin Manzon Allah SAW. Copy daga Shehul Islami Aminu Bello