Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta fara rabon katinan zaɓe na dindindin ga masu rajista a mazaɓun zaɓe 8,809 a faɗin Najeriya.
Hukumar INEC ta ƙuduri aniyar mayar da katin kaɗa ƙura'a na din-din zuwa yankunan da sukai rajista kimanin Dubu takwas da ɗari takwas da Tara
Kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye shi ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya sanya ma hannu a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Yace za a fara karɓar katin zaɓe na daga ranar Juma’a 6 ga watan Janairu zuwa ranar Lahadi 15 ga watan Janairu a shekarar 2023 da muke ciki.
An ce ana da buƙatar duk wanda yasan ya sabunta katinsa na zaɓe ko yayi rajista ta katin zaɓe yaje ya karɓo, domin za a fara kaisu zuwa inda kowa yake kaɗa ƙuru'a.
Majiyar tace, ana kira ga duk waɗanda suka yi rajistar zaɓe waɗanda har yanzu ba su karɓi katin ba da su yi amfani da damar da aka baiwa kowa don zuwa ya karɓo kafin lokaci ya wuce.
An ce, duk wanda bai zo ya karɓa ba har 15 ga watan Janairun 2023 ya wuce saide yaje ma’aikatun ƙananan hukumomin hukumar ya karɓar, tin daga ranar 22 ga watan Janairu, daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na marece a kullum, sun ce har da ranakun Asabar da Lahadi kowa zai iya zuwa ya karɓa.
Kwamishinan zaɓen yace, waɗanda suka nemi canja shekarun haihuwar su ko gyara sunayensu za su iya karɓar a wuraren da sukai rajistar da za su kaɗa kuri’a.
0 Comments
Post a Comment