A yammacin yau Asabar gobara ta tashi a hedikwatar yan sanda ta Kano da ke unguwar Bompai.


DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kudi, dakin taro, ofishin Kakakin hedikwatar,PPRO da kuma ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda (Admin) da sauransu.


An tattaro cewa wutar ta shafi dukkan ofisoshin da ke saman benen ginin, in banda ofishin kwamishinan.


“Mun yi kokarin kashe gobarar da ga ofishin Provost amma sai wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshin. ‘Yan kwana-kwana sun isa wurin ne kusan sa’o’i 2 bayan tashin gobarar,” wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN.