Wannan Zagayen, a gaban Masallacin Nabwi, nan ne gidan Abu Ayyub Ansari (رضي الله عنه) yake. A nan ne Annabi (SAW) ya fara zama na tsawon watanni da dama a kan hijirarsa zuwa Madina, yayin da ake gina masallacin Nabwi da dakunan matansa.


Lokacin da Annabi (SAW) ya shiga Madina sai ya ce wa mutane su bar taguwarsa ta bi hanyarta domin “Allah ya shiryar da ita”. Duk musulmi sun so ya kwana a Gidansu. Daga karshe rakumin ya durkusa, amma Annabi (SAW) bai sauka ba. Dabbar ta sake tashi tsaye, ta yi gaba da dan nisa, sannan ta koma ta durkusa a daidai inda a ka gina masallacin Nabwi a nan.


Kusa da wurin da rakumin ya durkusa Akwai gidan Abu Ayyub Ansari (رضي الله عنه) ya yi gaggawar dauke sirdi daga rakumin ya kai shi gidansa. Sai Annabi (SAW) ya ce cikin raha, “ Wajibi ne mutum ya bi sirdinsa , ya tafi tare da Abu Ayyub. Asad bn Zurara ( رضي الله عنه ) ya rik'e rumfar, sai aka ba shi damar kula da rakumin.


Cikakken suna Abu Ayyub Ansari (رضي الله عنه) shi ne Khalid bn Zaid bn Kulayb. Kabarinsa na nan a birnin Istanbul inda aka karrama shi da shahada a lokacin da aka yiwa Konstantinoful kawanya a halifancin Mu'awiyah (رضي الله عنه) a shekara ta 48 bayan hijira.


Saliadeen Sicey