Gembu Jihar Taraba Najeriya.
Gembu birni ne, da ke a yankin Duwatsun Mambilla, a Jihar Taraba, a Nijeriya. Ita ce hedikwatar karamar hukumar Sardauna (tsohuwar "Mambilla") a jihar Taraba.
Mutanen Mambilla ko Mambila na Najeriya suna zaune a tudun Mambilla. Kadan daga cikin 'yan ci-rani na Mambilla sun tashi daga duwatsun Mambilla zuwa filin Ndom da ke gefen Kamaru na kan iyakar kasa da kasa da kuma wasu kananan kauyuka, kamar sabuwar Namba, da ke kan arewa zuwa garuruwan Gashaka da Banyo.
Mambila na Zaune a matsakaita tsayin kusan mita 1,348 (4,423 ft) sama da matakin teku, yana daga cikin manyan biranen Najeriya.
Tarihi
An yi imani tun da dadewa cewa mutanen farko na mazaunan Duwatsun Mambilla su ne zuriyar kakannin Bantu. mutanen Bantu waÉ—anda suka zauna a Gembu ta zamani bayan faÉ—aÉ—ar Bantu a faÉ—in Afirka daga 4000 zuwa 3500 Kafin Haihuwar Annabi Isa AS
Dalilin Da zai sanyaku zuwa mambila
1, Garin yafi ko'ina matan fulani kyawawa
2, Dutsen Mambila yana Jahar Taraba kuma shine wuri mafi sanyi a Najeriya baki daya. Akasarin yara da ke tasowa a yankin ba su taɓa ganin na'urorin da ke bayar da sanyi a zahiri ba sai dai a talabijin ko kuma litattafai.
Gembu a ranar hudu ga watan Satumban shekarar 2021, yanayin sanyi ya kai maki 17 digiri selshiyos.
Shi ma shafin da ke wallafa bayanai na intanet Wikipedia ya tabbatar cewa ƙauyen Dorofi da ke kan tsaunin na Mambila shi ne yanki mafi sanyi a Najeriya.
Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin daga wani ƙauye da ake kira Mayo Selbe da ke karamar hukumar Gashaka za ka hangi tsauni mai tudun gaske lulluɓe da koren ciyayi da bishiyoyi da hazon ƙanƙara iya hangenka.
Daga wannan ƙauyen ne yanayi ke sauyawa daga zafi zuwa sanyi ko kuma sanyi zuwa ɗan karen sanyi.
Kana isa kan tsaunin daga garin Maisamari har zuwa sauran ƙauyuka da suka yi iyaka da jamhuriyar Kamaru za ka iske kusan kowa ya yi shigar maganin sanyi.
Za ka ga mutane da manyan rigunan sanyi da ake kira "Kuntu" da hulunan sanyi da takalma sau ciki domin maganin sanyi.
3, Saboda sanyi yasa mutanen wurin basa amfani da Firji, AC, ko fanka, domin duk wani nau'in kayan sha ko yaushe da sanyin sa.
4, kusan Kowa a garin ya iya fillanci duk dacewa manyan yaruka da kabilu 4 ne a yankin wanda suka hada da Mambilawa, Fulani, Panso da Kakah.
5, Hotel yanada araha a yankin domin akuwai dakin ₦1500
6, Garin yana da arzikin duwatsun daimond da blue sapaya, kana sunada arziƙin shanu shi yasa nama yake da araha a yankin.
7, Sunada nau'in kayan itace da nau'in abinci daban-daban har da wanda baka taba ganiba balle ci, wanda suka hada da piya, ayaba, chanis apple, mangoro, bulumji, deppi, dankalin turawa, samaije da sauransu, gwaiba kam tun a hanya zaka tsaya ka tsinka a hanya.
8, kauyukan da suke da kyawawan mata a dutsen mambila su hada da, Kakara, Leme, Yarimaru, Mayo-ndaga, Dorofi, Nguroje, da Galadima.
9, Dutsen yafi ko ina yawan itacen zaiti a Najeriya
10, Babu sauro a garin.
11, Manyan garuruwa da suke kan dutsin mambila sun hada da, Gembu, Nguroje, Mayo-ndaga (dago cede) da Mai samari.
0 Comments
Post a Comment