Fitacciyar mawaƙiyar nan Maryam Aliyu Muhammad, wadda aka fi sani da Maryam Bakassi ta ce, ƙofa a buɗe take ga duk mai son aurenta tsakani da Allah.


Bakassi ta kuma bayyana yadda take samun tsangwama daga wasu mutanen na cewa tana Æ´ar Kannywood amma take rufe jikinta ruf.


Kafin ta soma Waƙa Bakassi ta kasance mai yin amshi ga manyan mawaƙa.


Daga cikin waƙoƙin da ta yi amshi suka yi fice akwai waƙar nan ta "Kowa ya kauce kai ne kaɗai a hanyata..." da kuma "Hasashena ya tabbata gamu a tare cikin soyayya".


Zabiyar ta bayyana hakan ne a tattaunawarta da filin Fitattun Mawaƙa na Dala FM Kano.