Dede Koswara ya mutu ne a ranar 30 ga Janairu, 2016 , yana da shekaru 44, a Asibitin Hasan Sadikin, Bandung, Indonesia, daga jerin matsalolin lafiya da suka shafi yanayinsa.


Dede Koswara wanda kuma aka sani da "Man Tree", wani kafinta ne dan kasar Indonesiya Wanda Ya Gamu Da Cutar  (epidermodysplasia) A Likitance Wacce Ke Haifar da tsiro mai ciwo mai kamada bishiya.


Dede Koswara yana cikin koshin lafiya tun daga haihuwarsa har yarintarsa. Yana da shekaru goma, ya fara samun tsiro a kusa da gwiwarsa da ya ji rauni, wanda daga bisani ya girma a gabobinsa da fuskarsa. 


Bai iya samun maganin cutar ba kuma da farko ya yi Æ™oÆ™arin cire É—aya daga cikin manyan tsiron duk da haka Tsiron É—in ya sake komawa. 


Ya yi Æ™oÆ™ari ya yi rayuwa Kamar kowa, yayi aiki a matsayin mai sana'a. Ya yi aure yana da shekara 18 kuma ya haifi ‘ya’ya biyu. Tsiron sun ci gaba da girma ba tare da tsayawa ba, wanda a Æ™arshe ya kasance baya iya komai sai an taimaka masa.


Da yake Baya iya komai Gashi Ya Rasa aikinsa, matarsa ​​ta rabu da shi, kuma aka raba shi da ’ya’yansa.


Iyayensa sun ba shi shawarar ya zauna tare da su, don Su Taimaka masa, Daga baya wani mai Shirya Wasan Nune-Nune ya É—auke shi aiki don zama wani É“angare na nuna Shi  a tafiye-tafiye Don Samun kudi.


A cikin Nuwamba 2007, wani bidiyo game da Dede Koswara ya bayyana a Intanet. An ba da labarinsa a kan Tashar talabijin ta TLC a cikin Labarun Masu Ban Mamaki ( Mutane masu ban mamaki ) a cikin shirin "Half Man Half Tree". 


A cikin watan Agusta 2008, an yi masa aiki har sau tara amma Duk da haka  kashi 95% na Tsiron Bishiyar Yana nan.


Kusan kilogiram 6 (13 lb), aka cire shi ta hanyar tiyata. 


A wannan lokacin, lafiyarsa ta inganta sosai har ya sake samun amfani da hannayensa da Æ™afafu. Duk da haka, tsiron Suka sake  girma kuma an sanar da shi cewa ana bukatar Ayi masa tiyata sau biyu a shekara don rage cututtukan.


Dede Koswara ya mutu ne a ranar 30 ga Janairu, 2016, yana da shekaru 44, a Asibitin Hasan Sadikin , Bandung , Indonesia , daga jerin matsalolin lafiya da suka shafi yanayinsa.


Bashi kadai Bane Da Akwai Masu Irin Wannan Cutar Da Yawa A Duniya.