WAIWAYE:
Hotunan Abubakar Muhammad Barinjimi dalibi dan shekara 88 ya dauki hankulan abokan karatunsa da sauran jama’a, yayin da ya shiga aji a makarantar Firamare ta Model ta Hadin Gwiwar Najeriya da Masar da ke Kano, (Nigeria-Egyptian Model School).
Muhammad Barinjimi talaka ne amma yana da kyawawan buri don neman ilimi yayin da yake kusantar shekaru É—ari.
Burinsa dai shine ya yi digiri na uku a ilimin tauhidi.
Dalibai ’Yan uwansa da ke wannan makaranta yawancinsu 'yan shekara bakwai ne.
Dattijon dai ya shiga makarantar ne shekaru uku da suka gabata, inda a lokacin ne aka dauki hotunan.
Daga Saliadeen Sicey
0 Comments
Post a Comment