Ina magana ne da masu amfani da Normal WhatsApp, domin nasan tabbas da yawa sunsha faɗawa irin wannan matsalar, zakuyi Chats mai muhimmanci washe gari kuna hawa WhatsApp musamman idan Whatspp ɗin yayi expired zaku nemi chats naku ku rasa, ko kuma kanaso ka canza wayarka kana tunanin rasa Chats ɗinka na WhatsApp, gashi da zaran ka canza wayar kana tura WhatsApp a sabuwar wayar da kasiya ɗin kana buɗewa zakaga babu Messages ko ɗaya.


To In sha Allah akwai yadda zakayi daga yau ko ka canza waya kana saka WhatsApp naka a wata wayar duka Chats, Hotuna da Videos na WhatsApp ɗinka zasu dawo zaka gansu.


Farko zaka shiga WhatsApp naka sai kaje kai tsaye zuwa Setting na WhatsApp ɗin, daganan sai ka duba wurin da aka rubuta "Chats" sai ka danna wurin bayan ya buɗe zakaga Options da yawa sai kaje wurin da aka rubuta "Chats Backup" kana shiga zai baka Options da Notice akan Backup ɗin, to daman yadda backup ɗin yake shine zamu ƙwashe Chats ɗin namu ne da duk saƙonnin mu na WhatsApp zuwa Google Drive namu a cen ne zamu adana sakonnin namu, dan haka a wurin zakaga wurin da zaka sanya Email Address naka, bayan ka saka kuma zaga wurin da aka rubuta "Backup To Google Drive" kana danna wurin zai tambayeka shin kanason a dinga yi maka Backup ɗin kullun ne ko kuma duk bayan sati ɗaya ko wata ɗaya, ma'ana idan kace duk kullun kakeso to duk Chats ɗin da kayi a duk rana zasu tura chats ɗin a Google Drive ɗinka kai tsaye, kaga kana canza waya a ranar ma zaka samu Chats naka na ranar, idan kabarshi sai sati-sati, shima idan katashi canza waya sai ka duba idan satin yaje ƙarshe sai ka canza saboda kasamu Chats ɗinka na gabaɗaya satin haka zalika shima idan a wata ne ka seta shi dau sai ƙarshen wata amma nafi bada shawarar ka seta shi a duk kullun ayi maka Storing Data ɗinka a Google Drive naka zaifi sauƙi.


Note: Ga hotunan matakan da zakabi wurin shiga wannan tsarin a kasa, Allah yataimaka..🙏


© Salisu Abdurrazak Saheel