Jam'iyyar NNPP ta zama babbar Jam'iyyar adawa a jihar Gombe, inda ta karbi matsayi na biyu a Majalisar Dokoki ta jihar.
Biyo bayan canja sheka da Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaltungo East, Hon Bashir Yakubu Barau yayi zuwa jam'iyyar ta NNPP, a yanzu yawan yan majalisun jiha da NNPP take dasu ya wuce wanda PDP take dasu a majalisar.
Kafun wannan cigaba, Jam'iyyar NNPP da PDP suna da yan majalisu guda uku-uku, amma yanzu NNPP tasha gaban PDP da Dan majalisa daya.
Yanzu dai za'a sauce dan PDP daga matsayin MINORITY LEADER, za'a nada Dan NNPP a majalisar.
0 Comments
Post a Comment