. 


A Rana Mai Kamar Ta Yau 11 Ga Watan Junairu 630 Annabi Muhammad (SAW) da mabiyansa sun ci birnin Makkah Kuraishawa sun mika wuya.


630 CE: Annabi Muhammadu (SAW) ya dawo Makka tare da dimbin mabiyansa. Ya shiga garin lami lafiya, kuma daga karshe duk ‘yan kasar sun karbi Musulunci. Annabi yana share gumaka daga cikin Dakin Ka'aba kuma ya mayar da ita ga bautar Allah Shi kadai.


A shekara ta 8 bayan hijira (630 miladiyya) Kuraishawa na Makka suka karya yarjejeniyar Hudaibya da Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar kashe wasu daga cikin mutanen kabilar Khuza wadanda Annabi ya yi yarjejeniya da su, a cikin kewayen Ka’aba mai alfarma.


Bayan haka, saboda wannan karya alkawari da Kuraishawan suka yi, sai Manzon Allah ya fara hada runduna da nufi tafiya Makka da nufin yakan kafi*rai, inda ya tara runduna mai yawan gaske suka nufi Makkan. 


Wata ruwayar ta ce Manzon (SAW) ya fita ne da rundunar tasa a ranar 2 ga watan Ramalana shekara ta 8 bayan hijira zuwa Makkan, yana mai tsara al'amurran don kada yakin ya faru a cikin garin Makka saboda Haramin Allah ne.


Koda kafi*rai suka ga wannan runduna ta Manzon Allah (SAW) sai suka tsorata, Abu Sufyan ya mika wuya, ya karbi kalmar shahada saboda tsoron da dimautuwan da yake ciki. 


Don haka sai Manzon Allah (SAW) ya umurci Abbas bn Abdul Mutallib da ya tsaya tare da Abu Sufyan a inda Rundunar Ubangiji (Sojojin Musulmi) suke wucewa don ya ga girman Musulunci da idanuwansa. Lokacin da Abu Sufyan ya ga rundunar musulmi tana wucewa sai ya ce: "Lalle dan dan'uwankan nan (wato Manzon Allah) ya zama babban sarki". Nan take sai Abbas ya amsa masa da cewa: "Kaiconka! Ai wannan annabci kenan".


Ta haka ne Manzon Allah (SAW) ya sami wannan babban nasara, ya shiga garin Makka yana mai daukaka da kuma samun nasara ba tare da yaki ko zubar da jini ba. Yana mai kaskantar da kai ga Ubangijinsa, mai neman gafara da kuma godiya ga Ubangijinsa.